Saturday, 19 May 2018

INA MA'AURATA MASU HUSUMA?

INA MA'AURATA MASU HUSUMA?
*********************************
Babu Shakkah da yawa daga cikin Ma'aurata dayawa basu san hakkokin da shari'a ta rataya musu akan wuyansu.
Kuma Rashin Sanin wayannan Hakkokin su suke rura wutar gaba ko fada a cikin Gidajen Da yawa daga ma'aurata.
Farko fari kamata yayi ma'aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora akansu tun gabanin akai ga zamantake war Auren.
In shaa Allahu ZAUREN-MANAZARTA zaiyi kokarin Zakulo wayannan Hakkoki domin dukan mu ma amfana dasu.
HAKKOKIN MATA MIJINTA.
-Daga Cikin Hakkokin Mata akan Mijinta akwai ciyarwa da tufatarwa.
Hadisi ya tabbata daga Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (saww) ya ce, Dinaran da ka ciyar da shi fisabilillah, da kuma dinaran da ka 'yanta bawa da shi, da dinaran da ka ciyar da miskini da shi, da kuma dinaran da ka
ciyar da iyalinka, sai Manzon Allah (saww) ya ce, To, mafi girman lada a cikin wadannan shi ne dinaran da ka ciyar da iyalinka da shi.
Don Haka Yana da Yau Miji ya san Cewa, Ciyarda matarsa da iyalinsa yana bashi dinbin lada me yawan gaske.
Haka kuma Hadisi ya tabbata daga Mu’awiyyatul Kushairi (RA) ya ce Wata Rana Na Tambayi Manzon Allah (saww) Cewa, "Shin mene ne hakkin matar daya daga cikinmu a kansa? Sai Manzon Allah (saww) ya ce: ka ciyar da ita, idan ka ci, kuma ka tufatar da ita, idan ka tufata, kuma kada ka doke ta a fuska, kuma kada ka munana mata, kuma kada ka kaurace mata sai a cikin dakinta"
-Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, ya rika yi mata kyakkyawan zato.
Domin mummunan zato shi ne yake kawo rashin zaman lafiya da rigingimu a cikin gida. Sai dai idan abin da yake zaton ya bayyana, ko kuma ya dogara da wata babbar hujja da zai kare kansa a nan duniya da kuma gobe Qiyama.

MUTANE 3 DA BAZA SU SHIGA ALJANNA BA

MUTANE 3 DA BAZA SU SHIGA ALJANNA BA
*************************************
Abdullahi Bin Umar (RA) Yace, Manzon Allah (saww) Yace, Mutum 3 Ba zasu shiga Aljanna ba, Sannan kuma Allah (swt) ba zai dube su ba a ranar gobe Qiyama.
Na farko Mutumen da baya yiwa Mahaifansa Biyayya, Na Biyu Matar da ta kwaikwayi maza, Na Uku Da kuma Dayooth Shima baya shiga Aljanna.
Dayooth, Shine mutumen da baya kishin Iyalansa (kamar, matarsa, mahaifiyarsa da kuma Qanne ko yayyensa Mata).
Imamu Ahmad Ya Ruwaito Shi.
Ya Allah ka tsare dalibban Zauren-Manazarta da su da dukkan Musulmi da Fadawa a cikin daya daga wayannan Mutane.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU
**************************************
Wayannan Ayoyin Sune ayoyin Da Aljannu basa so, haka kuma wannan ayoyi waraka ne Ga kowane ciwo.
1. SURATUL FATIHA: Ankarbo hadisi daga Kharijah dan sult daga baffansa yace: Nazo gun Manzon Allah (saww) nayi masa sallama sai ya amsamin, sai na riski wasu mutane suna tareda wani mutum mahaukaci, sai dangin wannan mutumin suka cemin mun samu labarin abokinka (ko abokinku) yazo da
alkhairi, shin awurinka akwai wani abu da zaka yi ma wannan ya warke?
Sai yayi masa Ruqyah (addu'ah) da Suratul fatiha, sai Allah ya bashi lfy. Sai suka bani akuya, sai nazo Gun Annabi (saww) na bashi labari sai yace min Shin, ka Karanta wani abu  banda wannan Surah?
Nace a'a, sai yace min hakika kaci daga ruqyah ta gaskiyah, wato kayi magani da abinda shine mafi dacewa da inganci.
A duba a Abu-dawud hadisi mai
lamba 3420, da Nisa'i mai lamba 1032. Albani ya inganta wannan hadisin.
2. SURATUL BAQARAH : Annabi (saww) yana cewa:KADA KA
MAIDA GIDAJENKU MAKABARTA, DOMIN SHAIDANU BASA ZAMA GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL-BAQARAH.
A duba a Sahihu muslim 6/67 da kuma Tirmizi 5/157.
3. SURATUL IKHLAS DA FALAQ DA NAS: An karbo daga Uqbatu dan Aamir (RA) yace, ina rike da
linzamin abin hawan Annabi (saww) a wurin wani yaki, sai yace min ya Uqbatu fadi! Sai na
saurari Annabi, sai ya kara cemin fadi ya uqbah!! Sai nayi shiru ina saurare, sai yakara
fada har sau 3, sai na ce mezan fada ya rasulullah (saww)?
Sai yace min ka karanta Qulhuwallahu ahada (har karshen surar ya karantamin) sannan falaq da nas har
karshe, da muka karanta su har karshe sai Annabi (saww) yace min: BABU WASU SURORI MASU
TSARI KAMAR WADANNAN).
A duba a Nisa'i Hadisi (8/250), Albani ya inganta hadisin.
Bayan wadannan Ayoyoin Babu shakkah ALKUR'ANI dukkansa Warakane, duk wata surah wadda take dauke da ambaton wani alkawari na ubangiji ko cika alqawari ga bayi sa, ko kuma ambaton wuta da aljannu da shaidanu kamar suratul Muminun,Yasin,Safat, Dukhan, Jinn, Hashr, Zalzalah, Qari'ah, Kafiruun, dasauransu duka ana karantasu wurin Ruqyah, musamman ga masu fama da
iska, ko sihiri.
DAGA CIKIN AYOYINDA AKE KARANTAWA YAYIN RUQIYAH DON WARAKA DAGA CUTUTTUKA NA SIHIRI, ISKA DA LALURA WADDA AKA KASA GANE MAGANINTA AKWAI:
-Ayata ta 36 cikin suratul fusilat.
-Ayatul kursiyyu (kamar yadda yazo akissar mutumin mai yiwa Abu-hurairah sata da daddare.(bukhar i 4/487)
-Ayoyi biyu na karshen Suratul baqarah,kamar yadda bukhari yafitar 6/323.
-Ayoyi ukku na cikin suratul A'raf (ayata 54 zuwa ta 56).
- Aya cikin suratu ali-imran (aya ta 18).
-Ayoyi hudu nacikin suratul muminun (ayata115 zuwa 118)
-Ayata ta 3 cikin suratul jinn.
-Ayoyi 10 na cikin suratus safat (ayata 1 zuwa 10).
-Ayata 21 zuwa ta 24 cikin suratul hashr.
-Ayata 31 zuwa ta 34 cikin suratul rahman.
-Ayoyi biyu nakarshen suratul qalmi (51 zuwa ta 52).
INSHA ALLAHU DUK WATA CUTA DA TA GAGARA MAGANI INDAI ANA KARANTA WADANNAN SURORI DA AYOYI ZA'A SAMU WARAKA.
IMAM IBN QAYYIM YACE: Duk wanda Alkur'ani bai warkar dashi ba to babu abinda zai
warkar dashi, Idan kuma Alkur'ani bai isar masa ba to babu wata isuwa da zai samu gun Allah.
Yaci gaba dace wa: Watarana ina a makka sai ciwo ya sameni sai na nemi mai magani na rasa bansamu wani magani ba da zanyi amfani dashi, sai na kasance ina yiwa kaina magani (ruqyah) da Suratul Fatiha sai naga tasirinta mai ban mamaki, nazamo ina dibar zamzam sai nakaranta fatiha na sha, sai gashi na samu waraka cikakka, har na zamo ina baiwa mutane magani akan hakan, kuma yana
amfanardasu.
Don Allah duk Wanda Ya Samu Wannan Rubutu ya tura shi a duka Contect dinsa da Groups dinsa ba tare da cire ko harafi daya ba (a rubutun) domin ya zamo sadakatur Jariya a garemu mu duka.
An Gabadar da wannan Darasi a Zauren-Manazarta Whatsapp tun Shekarar 2014 a watan August.
SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA Whatsapp

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

TAMBAYA TA 00113
********************
Salam, ALLAH ya gafarta Malam ina neman da ka taimaka ka sanar dani hanyar da AKE samun tazarar haihuwa a musulunce wacce bata da side effect bayan azalo, kamar yadda naga Kayi ishara da hakan a wani rubutu naka amma kace bazaka fasa ba saboda dalili Na Shari'a. ALLAH ya Sani ni da matata muna bukatar tazarar haihuwa saboda yanzu haihuwar ta hudu amma ko YAYE bata yi take samun wani cikin a takaice dai duk yaran hudu yanzu babu wanda ya iya yiwa kansa wani abu sai anyi masa kai hatta magana babu wanda cikin su ya iya sosai duk da cewa wannan halitta ce, in kuma gaskiya waccen hanyar bana sonta saboda side effect din ta, shi kuma AZALO duk Na gwada amma akwai sai mu wayi gari mu ga juna 2 ya shiga. Daga
jahiadmukhtar@gmail.com
AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam hakika tun lokacin da na kawo matsalolin allurar da ake yiwa mata domin tazarar haihuwa nake ta samu sakonni akan bukatar na bayyana wanda bashi da matsala a lafiyance.
Dalilin da yasa na ki bayyana shi a public saboda ban san ya abin zai kasance bane, domin nayi imani akwai daga cikin mata wayanda basa son su haihu da mazansu, akwai kuma wayanda nake tsoron su dauki abin suyi amfani da shi ta hanyar banza.
Amma in shaa Allahu yanzu zan gabatar da shi a bayyane, kuma ina rokon don Allah kada ayi amfani da shi ta hanyar da bata dace ba.
Da farko 'bangaren Namiji Idan yana bukatar tsayar da haihuwa zai nemi 'ya'yan Gwanda Ya rika cin su kullum har tsawon sati 3 to daga wannan sati 3 din in sha Allahu kwayayen da suke cikin maniyinsa zasu tsinke ta yanda ko sun hadu da kwayayen macce basu da karfin da zasu shigar da ciki.
Kuma zai ci gaba da cin 'ya'yan ne har sai lokacin da yake son maniyinsa ya dawo daidai, daga ya daina cikinsu kuma to shikenan kwayayensa zasu dawo lafiya qalau.
Ta 'bangaren Macce kuma za'a nemi Lemun tsami a hada da Ruwan lemu ayi matsi da shi kwana 5 da gama Al'ada in shaa Allahu a wannan watan ba zata 'dauki ciki ba.
Amma fa ina son ka sani komai kayi domin ka tsayarda haihuwa idan Allah bai so haihuwar ta tsaya ba sai an samu rabo.
Ina fatan zamu kula da kyau. In shaa Allahu da kadan kadan duk zan kawo ragowar dabarun tsayarda haihuwar.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
*********************************
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.
4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.
6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

NEMAN HAIHUWA

NEMAN HAIHUWA

TAMBAYA TA 00115
*********************
Assalamu Alaikum malam ina maka fatan alheri malam Don Allah ina neman taimakoka shekarata 10 rabu na da haihuwa saboda nasa implant sai da nayi shekara ban cire ba, to tunda na cire har yau ban samin ciki ba kuma nata zuwa asibiti babu cigaba kuma wata ran indan na fara alada na sai ya huce kwana 15 Don Allah malam ka taimaka min da magani na sami haihuwa nagode Allah yasa ka da alheri.
AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam. Nima ina miki fatan Alkheri ke da dukkanin 'yan uwa. Da yake baki min cikakken bayani ba.
Bayanin kuwa baki gaya min cewa, ke taba haihuwa ba ko baki taba ba. Domin indai har baki taba haihuwa ba kika saka Implant to kuwa keyi babban kuskure.
A koda yaushe abinda nake so nunawa masu son yin tsarin gayyade Iyali to su san cewa idan fa macce bata taba haihuwa ba to akwai matsala yinsa, haka ma wani lokaci yakan iya zowa wayenda suka saba haihuwa da matsala.
Abinda zakiyi anan shine ki nemi Man Albabunaj Ki rika matsi da shi, ki nemi Man Ha/Sauda ki rika shafawa a Goshin ki, Gadon bayanki, da kuma Kirjinki, wannan zai taimaka wa kwayayen ki.
Sannan ki nemi Zuma tatacciya marar hadi ki rika shan Cokali 1 da safe kafin kici komai.
Sannan ina mai tunatar da ke ki dukufa da yin Istigfari da yin sadaqa.
Imamu Abu Hanifa ya fitarda wani hadisi daga Sayyidina Jabir bin Abdullah (RA) Cewa, wani mutum daga cikin mutane madina yazo wajen Annabi (Saww) yace, Ya Ma'aikin Allah har yanzu Allah bai kaddareni da samun haihuwa ba.
Sai Ma'aikin Allah (Saww) yace, Ina ka baro Istigfari da kuma Sadaqa?
Daga wannan ranar mutumen ya rika yin sadaqa tare da yin Istigfari, ana haka kawai sai Allah ya albarkace shi da 'ya'ya har guda tara.
Don haka ga wayanda suke neman haihuwa wannan babbar fa'idace gareku maimakon kashe makuddan kudade wajen magani ku yawaita yin sadaqa da Istigfari. Allah kasa mu dace.
Wallahu A'alama.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

BAYA IYA RIKE FITSARI

BAYA IYA RIKE FITSARI

TAMBAYA TA 00116
*********************
Assalamu Alaikum dafatan na lafya? Malam Dan Allah ataimaka min wallahi Dan sister nane yatashi dayin fitsari ajikinshi yana tsaye kawai sai yayita fitsari kuma yace baya sanin yanayi kuma bayajin fitsari sai dai yaga yana fita kawai don shekaran shi 12yrs amma kawai fitsarin fita yakeyi kuma dayawa ba kadan ba,anje asibiti an mishi test wai basuga komai ba.
AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam lafiya Qalau nake da fatan kema da 'yan uwa duk kuna lafiya.
Matsalar rike fitsari ko kasa tsayawar fitsari matsalace da ta shafi mafitsarar mutum da kwakwalwansa. A duk lokacin da kwakwalwa ta kasa amsar sakon mafitsara to fa daga nan abubuwa biyu zasu iya faruwa.
Na farko kodai mutun ya kasa rike fitsarin, ko kuma mutum ya kasa fitarda wannan fitsarin. Shi yasa za'a ga jarirai da kananan yara suna yawan fitsarin kwance.
Saboda a lokacin kwakwalwansu bata iya karbar sakon da mafitsarar su take aikowa.
Don haka ku nemi Man Na'a Na'a Cokali 5, Man Zaitun Cokaki 6 da Man Ridi Cokali 5 ku hadesu a rika bashi Cokali 2 sau 3 kullum.
A nemi zuma mai kyau arika hadawa da ruwan zafi ana bashi da safe kafin yaci abinci.
Sannan ku nemi ganyen tami shashu a rika yi masa miya da shi yana sha, In shaa Allahu za'a dace. Allah ya amfanar damu.
WALLAHU A'ALAM
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

Wednesday, 16 May 2018

MAHAIFIYA MAI ABIN MAMAKI

MAHAIFIYA MAI ABIN MAMAKI
**********
Na tsaneta. tsana ta hakika har bana son naganta, aikinta shine dafa abinci ga malamai da dalibbai .domin ta tallafawa karatuna.
Akwai wata rana da ta je har ajin mu (Class) saboda ta ganni ta tabbatar da lafiya ta, "YA ZA'AYI TA MIN HAKA TAZO WAJENA BAYAN TA SAN YANDA NA TSANETA?" haka na fa'da a zuciya ta.
Lokacin da tazo ajin namu ta min magana amma nayi kamar banganta ba. Ta dage da yi min magana anan ne na juyo a fusace, na gaggaya mata ba'kaken maganganu masu zafi, Na fita ajin da gudu raina a 'bace.
Washe gari na shigo makaranta kenan sai na hadu da wani 'dan Class din mu nan take ya bu'da baki yana cemin, "Eeey Mahaifiyarsa ido 'daya ne da ita"
Anan naji kamar in yiwa kaina kabari saboda bakin cikin wannan magana da yayi min, nan take na juya na koma gida wajen Mahaifiyata nace da ita, "IDAN DAI DON KI SAKA ANA YIMIN DARIYA NE ME ZAI HANA MA KI MUTU IN HUTA DA KE"
Mahaifiyata dai bata ce min uffan ba, har na gama gaggaya mata magana na wuce abina.
Allah ya yini mai basira sosai da sosai kuma na dage da karatu babu kama hannun yaro.
Ana haka kawai sai Allah ya kawo wata kungiya a makarantar mu masu bawa yara masu basira scholar ship zuwa kasar waje domin yin karatu.
Aka yi jarabawa Allah ya bani sa'a naci jarabawar, anan ne aka 'dauke ni aka kaini kasar Singapore domin yin karatun nawa.
Da yake ni mutum ne mai basira da hikima Allah ya taimake ni har na samu kammala karatuna ban dawo ba, cikin taimakon Allah na samu aiki a cen Singapore din.
Topa daga nan ne na samu sa'a domin bada dadewa ba na mallaki gida nawa na kaina a kasar ta Singapore daga bisani na nemi mata a cen aka daura mana aure da ita.
Na 'dau shekaru da aure har Allah ya albarkace ni da 'ya'ya ina jin dadin rayuwa cikin iyalin nawa, kwatsam wata rana mahaifiyata tazo ziyarata a Singapore.
Ina zaune a falo 'dana na fari (my fist born) yana wasa, mata ta tana kitchin tare da 'dana na biyu, kawai sai naji mutum a kofar gida ma'ana yana so a bashi umurni ya shigo.
Nan take 'dana na fari ya ruga da gudu yaje ya bude kofar ai kuwa yana budewa sai ya fara kuka, nan da nan na iso kofar bada shiri ba (domin) in gani meke faruwa yake kuka.
Me zan gani kawai sai naga mahaifiyata a tsaye (ashe abinda ya saka 'dan nawa kuka ganinta da yayi da ido dayane).
Anan na fara yi mata kururuwa tare da ce mata, "YA ZA'AYI KIZO GIDANA KI TSORATA MIN 'DANA? MAZA KI 'BACE MIN DA GANI".
Mahaifiyar tawa cikin sanyin hali tace dani, "YI HAKURI A SHE NAYI KUSKUREN GIDA NE. ( MA'ANA, BA NAN NE NAKE NEMA BA)". ta fita ta yi waje. Ban san ya akayi tazo Singapore ba, ban kuma tambaye ta ya akayi ba bare har in bata ruwa da abinci.
Wata rana an shirya taro a makarantar da na fara karatu, sai aka gayyaceni.
Na tashi na shirya tsaf na yanki tacket din jirgi na sauka kasar mu, bayan sauka ta a kasar sai na yanke shawarar bari in tafi tsohuwar unguwar tamu.
Bayan naje unguwar sai na samu gidan namu a rufe, ba tare da bata lokaci ba na tambayi makwaftanmu labarin mahaifiyar tawa.
Sai suka gaya min cewa ai ta mutu tun kusan wata 2 da suka wuce. Banji wani ciwo ba lokacin da suka gayamin bare inyi hawaye.
Na juya haka sai suka ce min, ga wata takarda da tasa a rubuta mata a lokacin da take cikin rashin lafiya.
Na karbi takardar na fara warware wa a hankali, nan take na fara karanta rubutun da ke cikin takardar.
YA 'DANA!
A KO DA YAUSHE TUNANINKA NAKE, INA MAI BAKA HAKURI DA NAJE GIDAN KA A Singapore KUMA NA BAWA 'YA'YANKA TSORO, NAJI DADI KWARAI DA GASKE LOKACIN DA SHUGABAN MAKARANTARKU YA GAYA MIN ZAKA ZO TARO, SAI DAI KUMA KASH! BANDA LAFIYAR DA ZAN IYA ZUWA DOMIN IN GANKA.
INA BAKA HAKURI AKAN DARIYAR DA ABOKANANKA SUKE MA SABODA NI. HAKIKA ZAN GAYA MAKA WANI SIRRI WANDA BAKA SANI BA.
A LOKACIN DA KANA YARO KARAMI BAKA MALLAKI HANKALINKA BA KA SAMU HATSARI WANDA YA KAI HAR KA RASA IDO DAYA.
KASAN CEWA LIKITAN YACE ANA IYA SAKA MA WATA TAYI LAFIYA QALAU, NI KUMA A MATSAYINA NA MAHAIFIYA SHINE NA BAKA TAWA NI NA ZAUNA DA IDON 'DAYA.
INA FATAN ZAKA KULA DA JIKOKINA, ALLAH YA YIMA ALBARKA.
NOTE:-
﹏﹏﹏
Wannan Labarin ya faru da gaske a Kasar Nepal, Ina fatan Zamu kula da irin Soyayyar da iyayen mu suke mana.


Tuesday, 9 January 2018

MAGANIN KORAR ALJANI KOWANE IRI DAGA JIKINKA DAN ADAM

MAGANIN KORAR ALJANI KOWANE IRI DAGA JIKINKA DAN ADAM.
**********************************************************************************
Mun sha bayarda Wayannan Maganukka game da Aljannu a wannan Zauren, Ganin Bukatar haka muka ga sake gabatarda wannan Fa'idar domin taimakon Dalibbanmu na ZAUREN-MANAZARTA tare da sauran Al'ummar Musulmi duka. Hanya ta Farko karanta wannan Addu'ar bayan kowace Sallah, tare da karantawa lokacin kwanciya hadi da lokacin da aka tashi daga bacci.

ﺍﻋﻮﺫ ﺑﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ﻭﺑﻜﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﺎﻣﺎﺕ ﺍﻟﺘﻰ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯﻫﻦ ﺑﺮ ﻭﻻ ﻓﺎﺟﺮ، ﻭﺑﺄﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﺴﻨﻰ ﻛﻠﻬﺎ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻟﻢ ﺃﻋﻠﻢ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﻭ ﺫﺭﺍ ﻭﺑﺮﺍ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﻨﺰﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﻌﺮﺝ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺫﺭﺍ ﻓﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﺨﺮﺝ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻭﻣﻦ ﻃﻮﺍﺭﻕ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﺇﻻ ﻃﺎﺭﻗﺎ ﻳﻄﺮﻕ ﺑﺨﻴﺮ ﻳﺎﺭﺣﻤﻦ ﻭﻣﻦ ﺷﺮﻛﻞ ﺩﺍﺑﺔ ﺭﺑﻰ ﺍﺧﺬ ﺑﻨﺎ ﺻﻴﺒﻬﺎ ﺇﻥ ﺭﺑﻰ ﻋﻠﻰ ﺻﺮﺍﻁ ﻣﺴﺘﻘﻴﻢ .
TRANSLTRTION
****************
A'uzu bi wajhillahil karimi, Wabi kalimaatil lahil lati la yujawizuhunna barran wala fajiran, Wabi asma'illahil husna kulliha, ma alimtu minha Wa malam a'alam min sharri ma khalaqa, Wa zara'a wa bara'a, wa min sharri ma yanxilu minas sama'i, wa min sharri ma ya'aruju fiha, wa min sharri ma zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariqan yaɗruqu bikhairin ya Rahmanu. Wa min sharri kulli dáabbatin Rabbi akhixun bi
nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin Mustaqim.
FASSARA
**********
Ina neman tsaruwa da Zatin Allah Mai Daraja kuma da cikakken kalmominsa, waɗanda babu wani na kirki ko fajirin da zai Qetaresu, kuma da sunayen Allah kyawawa dukkansu waɗanda na sani daga cikinsu da waɗanda ban sani ba, daga sharrin abinda Ya halitta, kuma Ya fitar kuma Ya Qaga, kuma daga sharrin abinda yakan sauka daga sama, da kuma sharrin abinda ya kan hau cikinta, da kuma sharrin abinda ya fitar cikin ƙasa, da kuma sharrin abinda yakan fita daga gareta, kuma da fitinar dare da rana, kuma daga masu isowa da dare da rana sai dai mai isowa wanda zai iso da Alkhairi, Ya Mai Rahama, kuma daga sharrin dukkan dabba wadda Ubangiji Ya riƙeta da makwarkwaɗarta, hakika kan Ubangijina yana bisa Tafarki Madaidaici.

Hanya ta Biyu kuma itace a nemi tsabar habbatus Sauda, sai a karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin wannan tsabar, sai a dinga hayaki a dakin da ke kwana.
Sannan a nemi Wayannan Mayukkan Mane Ha/sauda, Man Zaitun, Man Albabunaj, Man Man tafarnuwa a hadasu wuri daya a karanta ayoyin Ruqiya A ciki a rika shan Cokali 2 sau 2 a rana kuma a rika shafawa lokacin kwanciya.

In Shaa Allahu za'a dace da Iznin Allah, Aljani zai gudu bada shiri ba.

Ya Allah ka tsaremu daga Sharrin Aljannu Mazansu da Matansu.

MUNA FATAN ZAKU TAYAMU WAJEN WATSA WANNAN SAKON

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA whatsapp.

NA TSORATA DA KALAMANNAN

NA TSORATA DA KALAMANNAN
*********************************
Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa: Idan mutum ya iso ga ranarsa ta qarshe a duniya, wacce ita ce ta farko a lahira, za a nuna masa dukiyarsa, ‘ya’yansa da aikinsa.
Zai dubi dukiyarsa ya ce: Wallahi na kasance mai nuna kwadayi kan ki matuqa, to me kika tanadar min? Sai ta ce masa: Ka sayi likkafaninka da ni.

Sai ya juya wajen ‘ya’yansa ya ce: Wallahi na kasance mai qaunarku iyakacin qauna, kuma
ina ba ku kariya iyakacin kariya, me kuka tanadar min? Sai su ce: Za mu raka ka zuwa kabarinka da rufe ka.
Sai ya dubi aikinsa ya ce: Wallahi ka kasance abu mai nauyi gare ni, ni na kasance mai qasqantar da kai gare ka, me ka tanadar min? Sai ya ce: Zan kasance maka abokin zaman cikin kabari da ranar da za a tashe ka, har a gabatar da ni da kai gaban Ubangijinka.

Subhanallahi 'Yan Uwa Yana da kyau mu duba ayukkan da muke yi mu gani dana sharri dana khairi wannan ya fayi yawa domin mu gyara.

Ya Allah ka saka ayukkan mu na Alkhairi su rinjayi na sharri.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

KISSAR HIKIMAR ANNABI IBRAHIM (As).

KISSAR HIKIMAR ANNABI IBRAHIM (As).
******************************
**********
A lokacin da aka haifi Annabi Ibrahim (As), Allah ya saka masa saurin girma a jiki domin kuwa kwana daya a wajensa kamar wata daya ne, Wata daya kuma kamar shekara, a cikin kwana goma sha biyar (15 days), ya iya tafiya da magana da hikima da basira.
Wata Rana Annabi Ibrahim (As) yana tare da Mahaifiyarsa, Sai Yace, mata, "Wanene Ubangiji na?", Sai tace masa, "Nice Ubangijinka", Sai Yace mata, Ke kuma waye Ubangijinki? Sai tace, Masa Mahaifinka, Sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Sai tace da shi, Namaruzu. Sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Sai tace bata sani ba.

Mahaifiyar Annabi Ibrahim taje ta sanar da mahaifinsa Cewa, Tana zaton wanda ake cewa zai cenja addinin wannan gari, tana ji wannan yarone da ta haifa. Lokacin da Azara (Mahaifin Annabi Ibrahim (As)) yaji haka sai yaje gurinsa. Da zuwansa Sai Annabi Ibrahim (As) yace da shi, Ya babana wanene Ubangijinka? Sai mahaifinsa yace, Mahaifiyarka, sai yace, ita kuma waye Ubangijinta? Sai mahaifin Annabi Ibrahim yace, Nine. Sai yace, Kai kuma waye ubangijinka? Sai yace, Namaruzu, sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Da mahaifinsa yaji haka sai ya mareshi ya gargade shi akan karya sake jin irin wayannan tambayoyin
Ikon Allah Wannan itace tsantsar baiwa tare da hikima, Ya Allah ka bamu fahimtar Addininka mu da 'ya'yan mu tare kuma da Aiki da umurninka.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

Don girman Allah ka turawa Wasu