Tuesday, 9 January 2018

KISSAR HIKIMAR ANNABI IBRAHIM (As).

KISSAR HIKIMAR ANNABI IBRAHIM (As).
******************************
**********
A lokacin da aka haifi Annabi Ibrahim (As), Allah ya saka masa saurin girma a jiki domin kuwa kwana daya a wajensa kamar wata daya ne, Wata daya kuma kamar shekara, a cikin kwana goma sha biyar (15 days), ya iya tafiya da magana da hikima da basira.
Wata Rana Annabi Ibrahim (As) yana tare da Mahaifiyarsa, Sai Yace, mata, "Wanene Ubangiji na?", Sai tace masa, "Nice Ubangijinka", Sai Yace mata, Ke kuma waye Ubangijinki? Sai tace, Masa Mahaifinka, Sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Sai tace da shi, Namaruzu. Sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Sai tace bata sani ba.

Mahaifiyar Annabi Ibrahim taje ta sanar da mahaifinsa Cewa, Tana zaton wanda ake cewa zai cenja addinin wannan gari, tana ji wannan yarone da ta haifa. Lokacin da Azara (Mahaifin Annabi Ibrahim (As)) yaji haka sai yaje gurinsa. Da zuwansa Sai Annabi Ibrahim (As) yace da shi, Ya babana wanene Ubangijinka? Sai mahaifinsa yace, Mahaifiyarka, sai yace, ita kuma waye Ubangijinta? Sai mahaifin Annabi Ibrahim yace, Nine. Sai yace, Kai kuma waye ubangijinka? Sai yace, Namaruzu, sai yace, Shi kuma waye Ubangijinsa? Da mahaifinsa yaji haka sai ya mareshi ya gargade shi akan karya sake jin irin wayannan tambayoyin
Ikon Allah Wannan itace tsantsar baiwa tare da hikima, Ya Allah ka bamu fahimtar Addininka mu da 'ya'yan mu tare kuma da Aiki da umurninka.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

Don girman Allah ka turawa Wasu

No comments:

Post a Comment