INA MA'AURATA MASU HUSUMA?
****************************** ***
Babu Shakkah da yawa daga cikin Ma'aurata dayawa basu san hakkokin da shari'a ta rataya musu akan wuyansu.
******************************
Babu Shakkah da yawa daga cikin Ma'aurata dayawa basu san hakkokin da shari'a ta rataya musu akan wuyansu.
Kuma Rashin Sanin wayannan Hakkokin su suke rura wutar gaba ko fada a cikin Gidajen Da yawa daga ma'aurata.
Farko fari kamata yayi ma'aurata su san hakkokin da ke
kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora akansu tun gabanin akai ga
zamantake war Auren.
In shaa Allahu ZAUREN-MANAZARTA zaiyi kokarin Zakulo wayannan Hakkoki domin dukan mu ma amfana dasu.
HAKKOKIN MATA MIJINTA.
-Daga Cikin Hakkokin Mata akan Mijinta akwai ciyarwa da tufatarwa.
Hadisi ya tabbata daga Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ce:
Manzon Allah (saww) ya ce, Dinaran da ka ciyar da shi fisabilillah, da
kuma dinaran da ka 'yanta bawa da shi, da dinaran da ka ciyar da miskini
da shi, da kuma dinaran da ka
ciyar da iyalinka, sai Manzon Allah (saww) ya ce, To, mafi girman lada a cikin wadannan shi ne dinaran da ka ciyar da iyalinka da shi.
ciyar da iyalinka, sai Manzon Allah (saww) ya ce, To, mafi girman lada a cikin wadannan shi ne dinaran da ka ciyar da iyalinka da shi.
Don Haka Yana da Yau Miji ya san Cewa, Ciyarda matarsa da iyalinsa yana bashi dinbin lada me yawan gaske.
Haka kuma Hadisi ya tabbata daga Mu’awiyyatul Kushairi (RA)
ya ce Wata Rana Na Tambayi Manzon Allah (saww) Cewa, "Shin mene ne
hakkin matar daya daga cikinmu a kansa? Sai Manzon Allah (saww) ya ce:
ka ciyar da ita, idan ka ci, kuma ka tufatar da ita, idan ka tufata,
kuma kada ka doke ta a fuska, kuma kada ka munana mata, kuma kada ka
kaurace mata sai a cikin dakinta"
-Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, ya rika yi mata kyakkyawan zato.
mace a kan mijinta, ya rika yi mata kyakkyawan zato.
Domin mummunan zato shi ne yake kawo rashin zaman lafiya da
rigingimu a cikin gida. Sai dai idan abin da yake zaton ya bayyana, ko
kuma ya dogara da wata babbar hujja da zai kare kansa a nan duniya da
kuma gobe Qiyama.
No comments:
Post a Comment