MAHAIFIYA MAI ABIN MAMAKI
**********
Na tsaneta. tsana ta hakika har bana son naganta, aikinta shine dafa abinci ga malamai da dalibbai .domin ta tallafawa karatuna.
**********
Na tsaneta. tsana ta hakika har bana son naganta, aikinta shine dafa abinci ga malamai da dalibbai .domin ta tallafawa karatuna.
Akwai wata rana da ta je har ajin mu (Class) saboda ta
ganni ta tabbatar da lafiya ta, "YA ZA'AYI TA MIN HAKA TAZO WAJENA BAYAN
TA SAN YANDA NA TSANETA?" haka na fa'da a zuciya ta.
Lokacin da tazo ajin namu ta min magana amma nayi kamar
banganta ba. Ta dage da yi min magana anan ne na juyo a fusace, na
gaggaya mata ba'kaken maganganu masu zafi, Na fita ajin da gudu raina a
'bace.
Washe gari na shigo makaranta kenan sai na hadu da wani
'dan Class din mu nan take ya bu'da baki yana cemin, "Eeey Mahaifiyarsa
ido 'daya ne da ita"
Anan naji kamar in yiwa kaina kabari saboda bakin cikin
wannan magana da yayi min, nan take na juya na koma gida wajen
Mahaifiyata nace da ita, "IDAN DAI DON KI SAKA ANA YIMIN DARIYA NE ME
ZAI HANA MA KI MUTU IN HUTA DA KE"
Mahaifiyata dai bata ce min uffan ba, har na gama gaggaya mata magana na wuce abina.
Allah ya yini mai basira sosai da sosai kuma na dage da karatu babu kama hannun yaro.
Ana haka kawai sai Allah ya kawo wata kungiya a makarantar
mu masu bawa yara masu basira scholar ship zuwa kasar waje domin yin
karatu.
Aka yi jarabawa Allah ya bani sa'a naci jarabawar, anan ne aka 'dauke ni aka kaini kasar Singapore domin yin karatun nawa.
Da yake ni mutum ne mai basira da hikima Allah ya taimake
ni har na samu kammala karatuna ban dawo ba, cikin taimakon Allah na
samu aiki a cen Singapore din.
Topa daga nan ne na samu sa'a domin bada dadewa ba na
mallaki gida nawa na kaina a kasar ta Singapore daga bisani na nemi mata
a cen aka daura mana aure da ita.
Na 'dau shekaru da aure har Allah ya albarkace ni da 'ya'ya
ina jin dadin rayuwa cikin iyalin nawa, kwatsam wata rana mahaifiyata
tazo ziyarata a Singapore.
Ina zaune a falo 'dana na fari (my fist born) yana wasa,
mata ta tana kitchin tare da 'dana na biyu, kawai sai naji mutum a kofar
gida ma'ana yana so a bashi umurni ya shigo.
Nan take 'dana na fari ya ruga da gudu yaje ya bude kofar
ai kuwa yana budewa sai ya fara kuka, nan da nan na iso kofar bada shiri
ba (domin) in gani meke faruwa yake kuka.
Me zan gani kawai sai naga mahaifiyata a tsaye (ashe abinda ya saka 'dan nawa kuka ganinta da yayi da ido dayane).
Anan na fara yi mata kururuwa tare da ce mata, "YA ZA'AYI KIZO GIDANA KI TSORATA MIN 'DANA? MAZA KI 'BACE MIN DA GANI".
Mahaifiyar tawa cikin sanyin hali tace dani, "YI HAKURI A
SHE NAYI KUSKUREN GIDA NE. ( MA'ANA, BA NAN NE NAKE NEMA BA)". ta fita
ta yi waje. Ban san ya akayi tazo Singapore ba, ban kuma tambaye ta ya
akayi ba bare har in bata ruwa da abinci.
Wata rana an shirya taro a makarantar da na fara karatu, sai aka gayyaceni.
Na tashi na shirya tsaf na yanki tacket din jirgi na sauka
kasar mu, bayan sauka ta a kasar sai na yanke shawarar bari in tafi
tsohuwar unguwar tamu.
Bayan naje unguwar sai na samu gidan namu a rufe, ba tare da bata lokaci ba na tambayi makwaftanmu labarin mahaifiyar tawa.
Sai suka gaya min cewa ai ta mutu tun kusan wata 2 da suka wuce. Banji wani ciwo ba lokacin da suka gayamin bare inyi hawaye.
Na juya haka sai suka ce min, ga wata takarda da tasa a rubuta mata a lokacin da take cikin rashin lafiya.
Na karbi takardar na fara warware wa a hankali, nan take na fara karanta rubutun da ke cikin takardar.
YA 'DANA!
A KO DA YAUSHE TUNANINKA NAKE, INA MAI BAKA HAKURI DA NAJE
GIDAN KA A Singapore KUMA NA BAWA 'YA'YANKA TSORO, NAJI DADI KWARAI DA
GASKE LOKACIN DA SHUGABAN MAKARANTARKU YA GAYA MIN ZAKA ZO TARO, SAI DAI
KUMA KASH! BANDA LAFIYAR DA ZAN IYA ZUWA DOMIN IN GANKA.
INA BAKA HAKURI AKAN DARIYAR DA ABOKANANKA SUKE MA SABODA NI. HAKIKA ZAN GAYA MAKA WANI SIRRI WANDA BAKA SANI BA.
A LOKACIN DA KANA YARO KARAMI BAKA MALLAKI HANKALINKA BA KA SAMU HATSARI WANDA YA KAI HAR KA RASA IDO DAYA.
KASAN CEWA LIKITAN YACE ANA IYA SAKA MA WATA TAYI LAFIYA
QALAU, NI KUMA A MATSAYINA NA MAHAIFIYA SHINE NA BAKA TAWA NI NA ZAUNA
DA IDON 'DAYA.
INA FATAN ZAKA KULA DA JIKOKINA, ALLAH YA YIMA ALBARKA.
NOTE:-
﹏﹏﹏
Wannan Labarin ya faru da gaske a Kasar Nepal, Ina fatan Zamu kula da irin Soyayyar da iyayen mu suke mana.
﹏﹏﹏
Wannan Labarin ya faru da gaske a Kasar Nepal, Ina fatan Zamu kula da irin Soyayyar da iyayen mu suke mana.
No comments:
Post a Comment