Saturday, 19 May 2018

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

TAMBAYA TA 00113
********************
Salam, ALLAH ya gafarta Malam ina neman da ka taimaka ka sanar dani hanyar da AKE samun tazarar haihuwa a musulunce wacce bata da side effect bayan azalo, kamar yadda naga Kayi ishara da hakan a wani rubutu naka amma kace bazaka fasa ba saboda dalili Na Shari'a. ALLAH ya Sani ni da matata muna bukatar tazarar haihuwa saboda yanzu haihuwar ta hudu amma ko YAYE bata yi take samun wani cikin a takaice dai duk yaran hudu yanzu babu wanda ya iya yiwa kansa wani abu sai anyi masa kai hatta magana babu wanda cikin su ya iya sosai duk da cewa wannan halitta ce, in kuma gaskiya waccen hanyar bana sonta saboda side effect din ta, shi kuma AZALO duk Na gwada amma akwai sai mu wayi gari mu ga juna 2 ya shiga. Daga
jahiadmukhtar@gmail.com
AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam hakika tun lokacin da na kawo matsalolin allurar da ake yiwa mata domin tazarar haihuwa nake ta samu sakonni akan bukatar na bayyana wanda bashi da matsala a lafiyance.
Dalilin da yasa na ki bayyana shi a public saboda ban san ya abin zai kasance bane, domin nayi imani akwai daga cikin mata wayanda basa son su haihu da mazansu, akwai kuma wayanda nake tsoron su dauki abin suyi amfani da shi ta hanyar banza.
Amma in shaa Allahu yanzu zan gabatar da shi a bayyane, kuma ina rokon don Allah kada ayi amfani da shi ta hanyar da bata dace ba.
Da farko 'bangaren Namiji Idan yana bukatar tsayar da haihuwa zai nemi 'ya'yan Gwanda Ya rika cin su kullum har tsawon sati 3 to daga wannan sati 3 din in sha Allahu kwayayen da suke cikin maniyinsa zasu tsinke ta yanda ko sun hadu da kwayayen macce basu da karfin da zasu shigar da ciki.
Kuma zai ci gaba da cin 'ya'yan ne har sai lokacin da yake son maniyinsa ya dawo daidai, daga ya daina cikinsu kuma to shikenan kwayayensa zasu dawo lafiya qalau.
Ta 'bangaren Macce kuma za'a nemi Lemun tsami a hada da Ruwan lemu ayi matsi da shi kwana 5 da gama Al'ada in shaa Allahu a wannan watan ba zata 'dauki ciki ba.
Amma fa ina son ka sani komai kayi domin ka tsayarda haihuwa idan Allah bai so haihuwar ta tsaya ba sai an samu rabo.
Ina fatan zamu kula da kyau. In shaa Allahu da kadan kadan duk zan kawo ragowar dabarun tsayarda haihuwar.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

No comments:

Post a Comment