NEMAN HAIHUWA
•
TAMBAYA TA 00115
*********************
Assalamu Alaikum malam ina maka fatan alheri malam Don Allah ina neman taimakoka shekarata 10 rabu na da haihuwa saboda nasa implant sai da nayi shekara ban cire ba, to tunda na cire har yau ban samin ciki ba kuma nata zuwa asibiti babu cigaba kuma wata ran indan na fara alada na sai ya huce kwana 15 Don Allah malam ka taimaka min da magani na sami haihuwa nagode Allah yasa ka da alheri.

AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam. Nima ina miki fatan Alkheri ke da dukkanin 'yan uwa. Da yake baki min cikakken bayani ba.
*******
Wa'alaykumus-Salam. Nima ina miki fatan Alkheri ke da dukkanin 'yan uwa. Da yake baki min cikakken bayani ba.
Bayanin kuwa baki gaya min cewa, ke taba haihuwa ba ko baki
taba ba. Domin indai har baki taba haihuwa ba kika saka Implant to kuwa
keyi babban kuskure.
A koda yaushe abinda nake so nunawa masu son yin tsarin
gayyade Iyali to su san cewa idan fa macce bata taba haihuwa ba to akwai
matsala yinsa, haka ma wani lokaci yakan iya zowa wayenda suka saba
haihuwa da matsala.
Abinda zakiyi anan shine ki nemi Man Albabunaj Ki rika
matsi da shi, ki nemi Man Ha/Sauda ki rika shafawa a Goshin ki, Gadon
bayanki, da kuma Kirjinki, wannan zai taimaka wa kwayayen ki.
Sannan ki nemi Zuma tatacciya marar hadi ki rika shan Cokali 1 da safe kafin kici komai.
Sannan ina mai tunatar da ke ki dukufa da yin Istigfari da yin sadaqa.
Imamu Abu Hanifa ya fitarda wani hadisi daga Sayyidina
Jabir bin Abdullah (RA) Cewa, wani mutum daga cikin mutane madina yazo
wajen Annabi (Saww) yace, Ya Ma'aikin Allah har yanzu Allah bai
kaddareni da samun haihuwa ba.
Sai Ma'aikin Allah (Saww) yace, Ina ka baro Istigfari da kuma Sadaqa?
Daga wannan ranar mutumen ya rika yin sadaqa tare da yin
Istigfari, ana haka kawai sai Allah ya albarkace shi da 'ya'ya har guda
tara.
Don haka ga wayanda suke neman haihuwa wannan babbar
fa'idace gareku maimakon kashe makuddan kudade wajen magani ku yawaita
yin sadaqa da Istigfari. Allah kasa mu dace.
Wallahu A'alama.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
No comments:
Post a Comment