KARE NA SADUWA DA ITA
.
TAMBAYA TA 00105
********************
As Salamu alaikum, Ina maka fatan Alkhairi Malam. Na samu email dinka a page din Zauren Manazarta na facebook. Don ALLAH ka taimaka min Ina cikin wani hali. Shekaru da suka wuce na gamu da wata larura na mugun makarkai kamar Naga qadangare jangwalagwada Nata bina da gudu ko na ganni cikin kogi cike da crocodiles ko na na ganni cikin maqabarta ko anyi mutuwa ga gawarwaki nan da yawa. Nayi fama da ciwon kai musamman maduga ta sannan a cikin mafarkin na Ina ganin wani mutum Baqi Qato mummunan gaske Sannan na taba mafarki wani baqin kare yana saduwa dani. Na nemi magani shekera da shekeru Amma har yanzu dai ban dace ba. Wadannan mafarkai nakan yi su Lokaci Lokaci Sannan wani Abu dake damu na shine Wlh Malam na rasa mijin aure duk wanda Ya fito Yana So na Sai magana ta lalace ko muyi ta samun matsala ko ma Ya tafi haka kurum ba ta tare da Mun yi fada ba. Abin Ya dame ni matuqa duk qanne na da qawaye na Sunyi aure hakan tasa na nemi karatu yanzu haka Ina qasar India Ina Masters dina. Don ALLAH ka taimaka min.
Nagode.

AMSA
*******
Wa'alaykumus Salam. Nima Inaa miki da daukacin al'ummar musulmi fatan Alkheri.
*******
Wa'alaykumus Salam. Nima Inaa miki da daukacin al'ummar musulmi fatan Alkheri.
Babu shakkah 'yar uwa dalili Biyu kawai ya isa muce Kina
tattare ne da Jinnul Ashiq (Namijin dare). Dalili na Farko yawan
mafarkan da kike na dabbobi da rashin samun tsayayyen Manemi.
Domin Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur'ani
da Sunnah, kamar cikin Majmu'ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah
da littafin Ash-shifa'u bil qur'an minal jinnu wash shayadini na Ridha
Ash-sharkawi da littafin Minhajul qur'an li'ilaj as-hir wal
massi as-shaidani suka ce,
massi as-shaidani suka ce,
Daga cikin alamomin da ke nuna samuwar Jinnul Ashiq ga 'ya
macce shine, Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin
mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wanda take jin kunya ko wata da bata
sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace 'yar uwarta ko kuma ma a siffar
wata dabba daban.
Don haka Wannan Mafarkin Saduwar kadai zai tabbatar mana da Cewa Wannan Shaitani ne ke tare dake.
Yazo a cikin Minhajul qur'an li'ilaj as-hir wal massi
as-shaidani Cewa, Idan Wannan aljani ya shiga jikin Macce za ta kasance
duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure
kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.
kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.
Amma Idan Aljanarce a jikin Namiji take takan hana shi
karatu ko ya fara ba zai gane ba, ko kuma inya gane ta hana shi karatun
ko ta dinga sa masa
wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure ko a ki shi ko shi ya ki, in ya
kama sana'a sai ya yi ta samun matsala.
wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure ko a ki shi ko shi ya ki, in ya
kama sana'a sai ya yi ta samun matsala.
Babu shakkah wannan Aljani yana da mugun tasiri da mugun kamu ga jikin 'yan adam kuma yana da wahala wajen maganin.
Da yake kece kina kasar India kuma a india bansan a inane
kike ba, amma idan kina Garin Telangana ko kusa da Garin in shaa Allahu
zan turo miki phone number Limamin Masallachin Makkah Masjid (Abdullah
Quraishi) dake garin a email dinki.
Ki samu kije tare da wata Muharramarki ko Qawarki kiyi masa bayani In shaa Allahu zai taimakeki.
Kafin nan ki nemi Ha/sauda da Man tafarnuwa da Man Zaitun
ki saka a zuma ki karanta suratul Baqara gaba dayanta a cikin tare da
suratul Jinni da Arrahaman Ki rika shan cokali 3 sau 3 kullum.
Sannan Ki nemi Garin Haltit Kina diban 'dan ka'dan kina shayi da shi duk zaki kwanta.
Haka kuma Ki kula da karanta addu'o'in Kariya da suka tabbata daga bakin Manzon Allah (saww), na shiga ban daki da
fita, da na lokacin kwanciya, da na sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM).
fita, da na lokacin kwanciya, da na sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM).
Sannan ki kula da cin Halat da kuma gujewa Haram, sannan ki
dauka wannan matsala jarabawa ce daga Ubangiji (swt), sannan ki sani
duk wanda kika gani duniyarnan akwai abinda ke damunsa (akwai inda Allah
ke jarabtarsa), babu wanda yake 100%.
Ina Rokon Allah ya Sauwaka Miki dake dani da dukkanin Al'ummar musulmi.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
THANKS
ReplyDeleteMungode Allah gafarta malam. nima ina da irrin wannan masala
ReplyDelete