MATA KU KARANTA ZAKUJI DADI
****************************** ***
Babu shakka akwai wata daraja Mai girma da Allah ya bawa matan Al'ummar Annabi (Saww).
******************************
Babu shakka akwai wata daraja Mai girma da Allah ya bawa matan Al'ummar Annabi (Saww).
Shin ko kuna da masaniyar cewa, Macce ce farkon wadda ta fara karbar addinin Musulunci Wato NANA KHADIJA matar Annabi (saww).
Ko kuna da labari akan macece ta fara yin shahada a musulunci SUMAYYAH Mahaifiyar Ammar Matar YASIR.
ko kuna da labari kan cewa, Macce ce farkon Wadda ta fara
zama mai bada fatawa bayan wafatin Manzon Allah (saww), NANA AISHA (RA).
Ko kuna da labari akan cewa, Macce ce tafi kowa Son Annabi (saww), 'yarsa NANA FATIMA (RA).
Ko kuna da labari akan Cewa, Macece ta fara sadaukarda komai da rayuwarta ga Addini KHANSA.
Ko kuna da labari akan cewa, daga cikin jaruman da duniya basa mantawa da su a kwai macce, wato Kawlah Bint Al-Azwar.
Hakika mata a cikin wannan Al'ummar suna da Girma da 'daukaka marar misali. Don mu girmama mata mu nuna musu so da kauna.
Ya Allah ka taimaki maza da matan mu. Amin.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
No comments:
Post a Comment