WASU MAGUNNA MASU BAN MAMAKI DAGA ZAUREN-MANAZARTA
****************************** ************
******************************
1. Karas (Carrot), Idan aka yanka Karas (gunduwa-gunduwa)
aka dubi wajen da aka yanke din da kyau za'a ganshi kamar kwayar cikin
ido.
Babu Shakkah Bincike ya nuna Cin Karas na bawa ido kariya tare da inganta glashin na ido.
2. TUMATUR (tomato), Idan aka yanka tumaturi a cikin sa
za'a ga yana dauke da gidaje guda hudu (4 chambers), Zuciyar dan adam ma
haka tana dauke da wayannan gidajen guda hudu (4 chambers).
Bincike ya nuna tumatur yana Inganta Zuciya tare da samar da Jini a duka sassan jiki.
3. INABI (grape), 'ya'yan Inabi suna kama da Kwayoyin da suke cikin jini masu bada kariya ga garkuwar jiki.
Bincike ya nuna yawan shan 'ya'yan Inabi na taimakawa gangan jiki tare da hana yaduwar kwayoyin cuta.
4. 'YA'YAN BAURE (Figs) suna kama da 'ya'yan Maniyin 'da Namiji.
Bincike ya Nuna 'ya'yan Baure na gyara maniyin 'da namiji, tare da kara yawan 'ya'yan Maniyin.
5. GYADA (Walnut), Idan aka 'bara ta za'a tarar da ita kamar Kwakwalwa.
Bincike ya nuna yawan mu'amula da ita yana bude kwakwalwa tare da sanya saurin rike abu.
Allah a cikin Alqur'ani Mai girma yana Cewa, SHIN WACCE DAGA NI'IMOMIN UBANGIJI KUKE KARYATAWA? (Suratul Rahman aya ta 13).
Duk Inda kasan kake da rauni a jikinka, Kwakwalwa ce, Ido ne to ka jaraba amfani da wayannan za'a dace.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
www.fb.com/zaurenmu
No comments:
Post a Comment