Saturday, 30 September 2017

NA TSORATA DA KALAMANNAN

NA TSORATA DA KALAMANNAN
*********************************
Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa: Idan mutum ya iso ga ranarsa ta qarshe a duniya, wacce ita ce ta farko a lahira, za a nuna masa dukiyarsa, ‘ya’yansa da aikinsa.
Zai dubi dukiyarsa ya ce: Wallahi na kasance mai nuna kwadayi kan ki matuqa, to me kika tanadar min? Sai ta ce masa:
Ka sayi likkafaninka da ni.
Sai ya juya wajen ‘ya’yansa ya ce: Wallahi na kasance mai qaunarku iyakacin qauna, kuma
ina ba ku kariya iyakacin kariya, me kuka tanadar min? Sai su ce: Za mu raka ka zuwa kabarinka da rufe ka.
Sai ya dubi aikinsa ya ce: Wallahi ka kasance abu mai nauyi gare ni, ni na kasance mai qasqantar da kai gare ka, me ka tanadar min? Sai ya ce: Zan kasance maka abokin zaman cikin kabari da ranar da za a tashe ka, har a gabatar da ni da kai gaban Ubangijinka.
Subhanallahi 'Yan Uwa Yana da kyau mu duba ayukkan da muke yi mu gani dana sharri dana khairi wannan ya fayi yawa domin mu gyara.
Ya Allah ka saka ayukkan mu na Alkhairi su rinjayi na sharri.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

No comments:

Post a Comment