Saturday, 30 September 2017

KARE NA SADUWA DA ITA

KARE NA SADUWA DA ITA
.
TAMBAYA TA 00105
********************
As Salamu alaikum, Ina maka fatan Alkhairi Malam. Na samu email dinka a page din Zauren Manazarta na facebook. Don ALLAH ka taimaka min Ina cikin wani hali. Shekaru da suka wuce na gamu da wata larura na mugun makarkai kamar Naga qadangare jangwalagwada Nata bina da gudu ko na ganni cikin kogi cike da crocodiles  ko na na ganni cikin maqabarta ko anyi mutuwa ga gawarwaki nan da yawa. Nayi fama da ciwon kai musamman maduga ta sannan a cikin mafarkin na Ina ganin wani mutum Baqi Qato mummunan gaske Sannan na taba mafarki wani baqin kare yana saduwa dani. Na nemi magani shekera da shekeru Amma har yanzu dai ban dace ba. Wadannan mafarkai nakan yi su Lokaci Lokaci Sannan wani Abu dake damu na shine Wlh Malam na rasa mijin aure duk wanda Ya fito Yana So na Sai magana ta lalace ko muyi ta samun matsala ko ma Ya tafi haka kurum ba ta tare da Mun yi fada ba. Abin Ya dame ni matuqa duk qanne na da qawaye na Sunyi aure hakan tasa na nemi karatu yanzu haka Ina qasar India Ina Masters dina. Don ALLAH ka taimaka min.
Nagode.
AMSA
*******
Wa'alaykumus Salam. Nima Inaa miki da daukacin al'ummar musulmi fatan Alkheri.
Babu shakkah 'yar uwa dalili Biyu kawai ya isa muce Kina tattare ne da Jinnul Ashiq (Namijin dare). Dalili na Farko yawan mafarkan da kike na dabbobi da rashin samun tsayayyen Manemi.
Domin Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur'ani da Sunnah, kamar cikin Majmu'ul fatawa na Shaikul Islam ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa'u bil qur'an minal jinnu wash shayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul qur'an li'ilaj as-hir wal
massi as-shaidani suka ce,
Daga cikin alamomin da ke nuna samuwar Jinnul Ashiq ga 'ya macce shine, Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wanda take jin kunya ko wata da bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar mace 'yar uwarta ko kuma ma a siffar wata dabba daban.
Don haka Wannan Mafarkin Saduwar kadai zai tabbatar mana da Cewa Wannan Shaitani ne ke tare dake.
Yazo a cikin Minhajul qur'an li'ilaj as-hir wal massi as-shaidani Cewa, Idan Wannan aljani ya shiga jikin Macce za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure
kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.
Amma Idan Aljanarce a jikin Namiji take takan hana shi karatu ko ya fara ba zai gane ba, ko kuma inya gane ta hana shi karatun ko ta dinga sa masa
wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure ko a ki shi ko shi ya ki, in ya
kama sana'a sai ya yi ta samun matsala.
Babu shakkah wannan Aljani yana da mugun tasiri da mugun kamu ga jikin 'yan adam kuma yana da wahala wajen maganin.
Da yake kece kina kasar India kuma a india bansan a inane kike ba, amma idan kina Garin Telangana ko kusa da Garin in shaa Allahu zan turo miki phone number Limamin Masallachin Makkah Masjid (Abdullah Quraishi) dake garin a email dinki.
Ki samu kije tare da wata Muharramarki ko Qawarki kiyi masa bayani In shaa Allahu zai taimakeki.
Kafin nan ki nemi Ha/sauda da Man tafarnuwa da Man Zaitun ki saka a zuma ki karanta suratul Baqara gaba dayanta a cikin tare da suratul Jinni da Arrahaman Ki rika shan cokali 3 sau 3 kullum.
Sannan Ki nemi Garin Haltit Kina diban 'dan ka'dan kina shayi da shi duk zaki kwanta.
Haka kuma Ki kula da karanta addu'o'in Kariya da suka tabbata daga bakin Manzon Allah (saww), na shiga ban daki da
fita, da na lokacin kwanciya, da na sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM).
Sannan ki kula da cin Halat da kuma gujewa Haram, sannan ki dauka wannan matsala jarabawa ce daga Ubangiji (swt), sannan ki sani duk wanda kika gani duniyarnan akwai abinda ke damunsa (akwai inda Allah ke jarabtarsa), babu wanda yake 100%.
Ina Rokon Allah ya Sauwaka Miki dake dani da dukkanin Al'ummar musulmi.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

MUTUM HUDU DA BA'A ANSAR SALLARSU

MUTUM HUDU DA BA'A ANSAR SALLARSU
*****************************************
1. Manzon Allah (Saww) yace, Idan Bawa Ya guji Maigidansa Wannan bawan Allah Baya karban sallarsa har sai ya dawo
hannun Maigidansa.
2. Da matar da Mijinta yake fushi da ita, Matar da mijinta yake fushi da ita, itama wannan mata sallolinta Allah baya karbar su, har sai mijinta daina fushi da ita, ya yafe mata.
3. Mutumin da yaje wurin boka, wannan mutumin shima Allah bazai amshi Sallar sa ba har tsawo kwana 40.
4. Da mutumin da yasha giya Allah ba zai karbi sallarsa ba shima har tsahon kwana 40.
Kuma bayan Rashim amsar wannan sallar ita kanta sallar zata rika tsinewa mutumen tare da Rokar masa tozarta.
Imamu Hakim Ruwaito shi kuma yace, Hadsin ya Inganta daga Shugabn halittu Manzon Allah (saww).
Ya Allah ka Tsaremu da Wannan Tabewa duniya da Lahira.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU
**************************************
Wayannan Ayoyin Sune ayoyin Da Aljannu basa so, haka kuma wannan ayoyi waraka ne Ga kowane ciwo.
1. SURATUL FATIHA: Ankarbo hadisi daga Kharijah dan sult daga baffansa yace: Nazo gun Manzon Allah (saww) nayi masa sallama sai ya amsamin, sai na riski wasu mutane suna tareda wani mutum mahaukaci, sai dangin wannan mutumin suka cemin mun samu labarin abokinka (ko abokinku) yazo da
alkhairi, shin awurinka akwai wani abu da zaka yi ma wannan ya warke?
Sai yayi masa Ruqyah (addu'ah) da Suratul fatiha, sai Allah ya bashi lfy. Sai suka bani akuya, sai nazo Gun Annabi (saww) na bashi labari sai yace min Shin, ka Karanta wani abu  banda wannan Surah?
Nace a'a, sai yace min hakika kaci daga ruqyah ta gaskiyah, wato kayi magani da abinda shine mafi dacewa da inganci.
A duba a Abu-dawud hadisi mai
lamba 3420, da Nisa'i mai lamba 1032. Albani ya inganta wannan hadisin.
2. SURATUL BAQARAH : Annabi (saww) yana cewa:KADA KA
MAIDA GIDAJENKU MAKABARTA, DOMIN SHAIDANU BASA ZAMA GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL-BAQARAH.
A duba a Sahihu muslim 6/67 da kuma Tirmizi 5/157.
3. SURATUL IKHLAS DA FALAQ DA NAS: An karbo daga Uqbatu dan Aamir (RA) yace, ina rike da
linzamin abin hawan Annabi (saww) a wurin wani yaki, sai yace min ya Uqbatu fadi! Sai na
saurari Annabi, sai ya kara cemin fadi ya uqbah!! Sai nayi shiru ina saurare, sai yakara
fada har sau 3, sai na ce mezan fada ya rasulullah (saww)?
Sai yace min ka karanta Qulhuwallahu ahada (har karshen surar ya karantamin) sannan falaq da nas har
karshe, da muka karanta su har karshe sai Annabi (saww) yace min: BABU WASU SURORI MASU
TSARI KAMAR WADANNAN).
A duba a Nisa'i Hadisi (8/250), Albani ya inganta hadisin.
Bayan wadannan Ayoyoin Babu shakkah ALKUR'ANI dukkansa Warakane, duk wata surah wadda take dauke da ambaton wani alkawari na ubangiji ko cika alqawari ga bayi sa, ko kuma ambaton wuta da aljannu da shaidanu kamar suratul Muminun,Yasin,Safat, Dukhan, Jinn, Hashr, Zalzalah, Qari'ah, Kafiruun, dasauransu duka ana karantasu wurin Ruqyah, musamman ga masu fama da
iska, ko sihiri.
DAGA CIKIN AYOYINDA AKE KARANTAWA YAYIN RUQIYAH DON WARAKA DAGA CUTUTTUKA NA SIHIRI, ISKA DA LALURA WADDA AKA KASA GANE MAGANINTA AKWAI:
-Ayata ta 36 cikin suratul fusilat.
-Ayatul kursiyyu (kamar yadda yazo akissar mutumin mai yiwa Abu-hurairah sata da daddare.(bukhar i 4/487)
-Ayoyi biyu na karshen Suratul baqarah,kamar yadda bukhari yafitar 6/323.
-Ayoyi ukku na cikin suratul A'raf (ayata 54 zuwa ta 56).
- Aya cikin suratu ali-imran (aya ta 18).
-Ayoyi hudu nacikin suratul muminun (ayata115 zuwa 118)
-Ayata ta 3 cikin suratul jinn.
-Ayoyi 10 na cikin suratus safat (ayata 1 zuwa 10).
-Ayata 21 zuwa ta 24 cikin suratul hashr.
-Ayata 31 zuwa ta 34 cikin suratul rahman.
-Ayoyi biyu nakarshen suratul qalmi (51 zuwa ta 52).
INSHA ALLAHU DUK WATA CUTA DA TA GAGARA MAGANI INDAI ANA KARANTA WADANNAN SURORI DA AYOYI ZA'A SAMU WARAKA.
IMAM IBN QAYYIM YACE: Duk wanda Alkur'ani bai warkar dashi ba to babu abinda zai
warkar dashi, Idan kuma Alkur'ani bai isar masa ba to babu wata isuwa da zai samu gun Allah.
Yaci gaba dace wa: Watarana ina a makka sai ciwo ya sameni sai na nemi mai magani na rasa bansamu wani magani ba da zanyi amfani dashi, sai na kasance ina yiwa kaina magani (ruqyah) da Suratul Fatiha sai naga tasirinta mai ban mamaki, nazamo ina dibar zamzam sai nakaranta fatiha na sha, sai gashi na samu waraka cikakka, har na zamo ina baiwa mutane magani akan hakan, kuma yana
amfanardasu.
Don Allah duk Wanda Ya Samu Wannan Rubutu ya tura shi a duka Contect dinsa da Groups dinsa ba tare da cire ko harafi daya ba (a rubutun) domin ya zamo sadakatur Jariya a garemu mu duka.
An Gabadar da wannan Darasi a Zauren-Manazarta Whatsapp tun Shekarar 2014 a watan August.
SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA Whatsapp
Email, zaurenmanazarta8@gmail.com

NA TSORATA DA KALAMANNAN

NA TSORATA DA KALAMANNAN
*********************************
Sayyidina Aliyu (RA) yana cewa: Idan mutum ya iso ga ranarsa ta qarshe a duniya, wacce ita ce ta farko a lahira, za a nuna masa dukiyarsa, ‘ya’yansa da aikinsa.
Zai dubi dukiyarsa ya ce: Wallahi na kasance mai nuna kwadayi kan ki matuqa, to me kika tanadar min? Sai ta ce masa:
Ka sayi likkafaninka da ni.
Sai ya juya wajen ‘ya’yansa ya ce: Wallahi na kasance mai qaunarku iyakacin qauna, kuma
ina ba ku kariya iyakacin kariya, me kuka tanadar min? Sai su ce: Za mu raka ka zuwa kabarinka da rufe ka.
Sai ya dubi aikinsa ya ce: Wallahi ka kasance abu mai nauyi gare ni, ni na kasance mai qasqantar da kai gare ka, me ka tanadar min? Sai ya ce: Zan kasance maka abokin zaman cikin kabari da ranar da za a tashe ka, har a gabatar da ni da kai gaban Ubangijinka.
Subhanallahi 'Yan Uwa Yana da kyau mu duba ayukkan da muke yi mu gani dana sharri dana khairi wannan ya fayi yawa domin mu gyara.
Ya Allah ka saka ayukkan mu na Alkhairi su rinjayi na sharri.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

IN GANTACCEN MAGANIN BASIR

MAGANIN BASIR
******************
Na sha yin bayani akan maganin basir amma har yanzu ina samun sako akan neman taimako game da basir, In shaa Allahu gashi.
Za'a nemi Garin Ruman a zuma acikin tatacciyar Zuma mara hadi a juyasu su hade sosai sai arinka shan karamin cokali 1 sau uku arana.
Wannan hadin maganin Yana Magani cutukka da Yawa kamar ulcer, basir, ciwon ciki, lalacewar ciki da sauransu.
Kuma Ya kansa, jikin mutum, yayi kyau Yayi karfi da Iznin Allah.
Allah ya kara mana Lafiya da Zama lafiya.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

MATA KU KARANTA ZAKUJI DADI

MATA KU KARANTA ZAKUJI DADI
*********************************
Babu shakka akwai wata daraja Mai girma da Allah ya bawa matan Al'ummar Annabi (Saww).
Shin ko kuna da masaniyar cewa, Macce ce farkon wadda ta fara karbar addinin Musulunci Wato NANA KHADIJA matar Annabi (saww).
Ko kuna da labari akan macece ta fara yin shahada a musulunci SUMAYYAH Mahaifiyar Ammar Matar YASIR.
ko kuna da labari kan cewa, Macce ce farkon Wadda ta fara zama mai bada fatawa bayan wafatin Manzon Allah (saww), NANA AISHA (RA).
Ko kuna da labari akan cewa, Macce ce tafi kowa Son Annabi (saww), 'yarsa NANA FATIMA (RA).
Ko kuna da labari akan Cewa, Macece ta fara sadaukarda komai da rayuwarta ga Addini KHANSA.
Ko kuna da labari akan cewa, daga cikin jaruman da duniya basa mantawa da su a kwai macce, wato Kawlah Bint Al-Azwar.
Hakika mata a cikin wannan Al'ummar suna da Girma da 'daukaka marar misali. Don mu girmama mata mu nuna musu so da kauna.
Ya Allah ka taimaki maza da matan mu. Amin.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

WASU MAGUNNA MASU BAN MAMAKI DAGA ZAUREN-MANAZARTA

WASU MAGUNNA MASU BAN MAMAKI DAGA ZAUREN-MANAZARTA    
******************************************
1. Karas (Carrot), Idan aka yanka Karas (gunduwa-gunduwa) aka dubi wajen da aka yanke din da kyau za'a ganshi kamar kwayar cikin ido.
Babu Shakkah Bincike ya nuna Cin Karas na bawa ido kariya tare da inganta glashin na ido.
2. TUMATUR (tomato), Idan aka yanka tumaturi a cikin sa za'a ga yana dauke da gidaje guda hudu (4 chambers), Zuciyar dan adam ma haka tana dauke da wayannan gidajen guda hudu (4 chambers).
Bincike ya nuna tumatur yana Inganta Zuciya tare da samar da Jini a duka sassan jiki.
3. INABI (grape), 'ya'yan Inabi suna kama da Kwayoyin da suke cikin jini masu bada kariya ga garkuwar jiki.
Bincike ya nuna yawan shan 'ya'yan Inabi na taimakawa gangan jiki tare da hana yaduwar kwayoyin cuta.
4. 'YA'YAN BAURE (Figs) suna kama da 'ya'yan Maniyin 'da Namiji.
Bincike ya Nuna 'ya'yan Baure na gyara maniyin 'da namiji, tare da kara yawan 'ya'yan Maniyin.
5. GYADA (Walnut), Idan aka 'bara ta za'a tarar da ita kamar Kwakwalwa.
Bincike ya nuna yawan mu'amula da ita yana bude kwakwalwa tare da sanya saurin rike abu.
Allah a cikin Alqur'ani Mai girma yana Cewa, SHIN WACCE DAGA NI'IMOMIN UBANGIJI KUKE KARYATAWA? (Suratul Rahman aya ta 13).
Duk Inda kasan kake da rauni a jikinka, Kwakwalwa ce, Ido ne to ka jaraba amfani da wayannan za'a dace.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
www.fb.com/zaurenmu