SAK'O ZUWA GA MATAYE MU
Kafin Zuwan Manzon Allah (saww), anyi wata baiwar Allah mai fasaha UMMAH
Bint Al-HARIS ita wannan matar ta kasance 'yar Kabilar BANIY SHAIBAN
ce.
Sunan Mijinta AUFU bin MUHALLAM AS-SHAYBANIY shi wannan
Miji nata ya kasance shugaba (Sarki) ne a cikin Kabilar su kuma shine
jagoransu. Suna da wata 'ya mai suna Ummu-iyaas, sai sarkin wani gari
mai suna kinda sunan wannan sarkin kuwa Alharis Bin Amru ya nemi auren
'yarsu mai suna Ummu-iyaas, sai kuma aka aurar masa ita, to a nan ne
mahaifiyar wannan amarya ta yi mata wasiyya da zamu gabatar muku a
wannan ZAUREN-MANAZARTA.
Kuma wannan wasiya da yawa maluma suna daukanta daga cikin mafifitan wasiyyoyi da aka yi ma 'ya mace lokacin aurar da ita.
Wannan Matar ta Fara da Cewa, "Ya ke karamar 'yata! Lallai
wasiyya da za'a iya barin gabatar da ita ga mutum don cikar ladabinsa to
da baza a yi miki ita ba sai dai ita (wasiyya) tunatarwa ce ga wanda ya
gafala, taimako ne ga duk mutum mai hankali. Da ace akwai matar da zata wadata ba sai ta yi aure ba;
saboda kasancewar iyayenta mawadata, da kuma son da suke mata; To da ke
ce kika fi dukkan mata bukatar barinsa (aure); sai dai kuma su mata an
halicce su ne don maza, kamar yadda don su (matan) aka halicci maza!
Taci gaba da Cewa, ! !Ya ke karamar 'yata! Lallai ke kin
riga kin rabu da wannan yanayin da kika fito daga cikinsa, kin kuma bar
sabon da kika fito daga cikinsa (ma'ana: kin bar gidan da aka haife ki,
sannan kika girma a cikinsa; gidan iyaye), kin tafi zuwa gidan da baki
sanshi ba, zuwa kuma ga abokin zaman da baki saba da shi ba, wanda ya
wayi gari za'a daura muku aure tare, zaki je ga wanda zai mallake ki; Don haka Ki zame masa
baiwa (mai bin umurni) Ina kyautata zato idan kika zamar masa baiwa shi
kuma zai zame miki bawa mai sauri amsawa Taci gaba da Cewa, Yake Karamar 'yata Ki ji sifofi goma daga gare ni; za su zame miki guzuri, kuma abin ambato a gidan miji;
NA FARKO DA NA BIYU: Ki yi abota da mijinki da wadatar zuci, ki kuma yi zamantakewa da shi cikin ji da biyayya. Ma'ana; Abota da wadatar zuci anan tana nufin duk abinda
mijinki ya kawo miki kada ki kushe abin, ki zama mai godia a gareshi duk
abinda ya kawo ko ya sayo miki.
NA UKU DA NA HUDU: Ki kiyaye mai idanunsa biyu zasu gani, da wanda hanci zai ji; kar ki yarda
idanunsa su ganki kina aikata mummuna, kada kuma hancinsa ya shanshani
wani abu face mafi dadin iska!
Ma'anar Ki kiyaye me idanunsa biyu zasu gani anan, tana
nufin, ta sanya ido akan abinda mijinta ke fara kallo idan ya dawo daga
ofis ko kasuwa,
Idan kafafuwanki yake kallo ki tabbatar kafin ya dawo ke wanke su ke gyarasu sosai
Idan kuma Kirjinki yake fara kallo sai ki yawaita kula da shi ki masa abinda zai rika dad'a masa sha'awar kirjin.
Idan kuma fuskarki yake fara kallo to ki tabbatar ke tsaftace ta kafin ya shigo gidan.
Ma'anar kada ki bari idanunsa ya ganki kina aikata munana
anan shine, Kada ki bari mijinki ya ganki kina satar masa kuddi da
sauransu. Ma'anar Kada hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin
iska anan shine, Kada ki bari mijinki yaji wani wari a jikin ki, ko a
bakinki ko a hamattanki da sassan wuraren da Wari ke fita.
NA BIYAR DA NA SHIDA: Kiyaye lokacin cin abincinsa, da kuma natsuwa a yayin barcinsa; saboda tsananin
yinwa na kunna bakin-wuta, yayin da shi kuma yanke barci ke sanya bacin
rai! Da tace, Ki kiyaye lokacin cin abincinsa, anan tana nufin
Idan har yana jin yunwa to ki kula kada ki taso masa da wata maganar
daban ko wani korafi (Complain) har sai kega ya ci Abinci ya koshi. Da tace, Ki natsu a lokacin baccin sa, anan tana nufin kada
mijinki yana jin bacci kice zaki takura shi da surutu, ko kuma nuna
biyan wata bukata.
NA BAKWAI DA NA TAKWAS: Ki kiyaye masa dukiyarsa, ki kuma kula masa da danginsa da iyalansa; saboda
kiyaye masa dukiya na daga kyawawan siffofi, shi kuma lura da danginsa
da iyalansa yana daga girmamawa Da tace, Ki kula masa da dukiyar sa anan tana nufin, Kada ki rika saka mijinki yana kashin kuddi da yawa. Ki kula da danginsa, anan tana nufin kada ki wulaqanta 'yan
uwansa domin Wulaqanta dangin miji na saka suji sun tsani mijin, shi
kuma daga karshe yaji ya tsane ki.
NA TARA DA NA GOMA: Kada ki yada sirrinsa, kuma kada ki saba ma umurninsa; saboda idan har kika yada sirrinsa to baza ki taba amintuwa da shi ba, in kuma ki ka saba umurninsa to kin tafasa kirjinsa!
Ma'anar Kada ki yad'a sirrinsa anan tana nufin, Kada
mijinki ya gaya miki wani muhimmin sirri kije ki gayawa wata, domin idan
har kika gayawa wata yaji to gobe zai rika gudun gaya miki wata magana.
Sai kuma ta cike wasiyyarta da fadin;
Ki kuma kiyayi yin farin ciki a lokacin da mijinki ke
cikin bacin rai, da bayyanar da bacin rai a lokacin da yake farin ciki;
saboda yin farin cikin mace lokacin bacin ran mijinta na daga sakaci da
jafa'i, yayin da shi kuma bata ranta a halin farin cikinsa zai gurbata
masa nasa farin ciki!
Kuma gwargwadon yadda kika kasance kike girmama shi,
gwargwadon yadda zai yi ta karrama ki (da kyautuka), kamar yadda
gwargwadon yadda kike masa muwafaka (ba gardama) gwargwadon jimawanki a
wajensa!
Kuma ki sani! Ba za ki isa ga samun abinda kike so ba;
har sai kin fifita yardarsa akan yardarki, da abinda yake karkata zuwa
gare shi akan naki; cikin duk abin da kika so, ko kika ki!
Daga karshe ta rufe da Cewa, ALLAH YA YI MIKI ZABIN ALKHAIRI.
A Duba a DA'IRATU MA'ARIFIL USRATIL MUSLIMAH (littafi na 54/ shafi na 180).
Ya 'yan Uwayen mu mata ku lura da kyau da wannan Wasiya da
kyau, hakika da duka matayen mu zasu kula da wayannan abubuwa da sun
mallake mazajen su. In Shaa Allahu zamu kawo kwatan kwacin Wannan shawara zuwa ga Maza. Wannan Sakon Yana Bukatar Watsuwa Ga sauran 'yan Uwa da Fatar ALLAH zai baku Ikon Isarwa kamar yadda na Isar.
SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.