MATA MU DAU DARASI DAGA NANA FATIMA (RA).
****************************** ******************
Manzon Allah (Saww) ya ce, Fatima Shugabar mataye ce baki daya. Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” ko kun san dalilin da yasa ta samu wannan matsayi da girma? To ku tsaya kuji.
******************************
Manzon Allah (Saww) ya ce, Fatima Shugabar mataye ce baki daya. Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” ko kun san dalilin da yasa ta samu wannan matsayi da girma? To ku tsaya kuji.
An hadisi ruwaito daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari (RA)
ya ce; Mun yi Sallar Asar tare da Manzon Allah (Saww), bayan Sallah muna
zaune tare da Manzon Allah (Saww), sai ga wani Dattijo ya zo ya je
wajen Manzon Allah (Saww) yake yi masa bayanin halin da yake ciki na
kunci na rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma kudi.Sai Manzon Allah (saww) ya ce masa; “Ga shi kuwa ba ni da wani abu da zan ba ka”
Sai ya ce masa; “Amma Ka tafi gidan Fatima”. Wannan Dattijo
sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (RA) da ya je gidan ya yi
sallama.
Bayan haka ya shida wa Sayyida Fatima (RA) ga halin da yake ciki na bai da abinci da
tufafi da kuma kuddi. A lokacin da ya zo Nana Fatima ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta dauko shimfidar da 'ya'yanta Hasan da Husain ke kwana, ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bukatarsa.
tufafi da kuma kuddi. A lokacin da ya zo Nana Fatima ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta dauko shimfidar da 'ya'yanta Hasan da Husain ke kwana, ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bukatarsa.
Sai Dattijon ya ce shi ba zai amsa ba, domin shi a
tunaninsa abin ba zai yi kima ba. To kasantuwar ya raina wannan abin da
aka ba shi, sai Nana Fatima ta shiga gida ta debe abin wuyanta, wato sarka, ta kawo masa.
Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah
(Saww), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah
(Saww) Fatima ta ba ni wannan sarkar a kan in sayar domin in biya bukatuna”.
Nan da nan Sai Manzon Allah (Saww) ya fashe da kuka, ya ce
yaya ko ba za ka samu biyan bukata ba, alhali Fatima ’yar Muhammad
Shugabar mataye ta ba ka.
Sai Ammar bin Yasir (RA) ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ka
ba ni izini in saye wannan abin wuyan”. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce
masa yana iya saye Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayarmasa da sakar? Sai ya ce masa; “Ni daiabin da nake bukata kayan abinci
da tufa ko da kuwa daya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da daya ne da zai
kai ni garinmu”. Sai Ammar ya hama masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi kudi Dinare 20.
Bayan haka sai shi Dattijon ya zo wajen Manzon Allah
(Saww), sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa; “Ka samu abinci da tufan?”
Sai Dattijon ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ai ni yanzu na zama mawadaci”.
Saboda farin ciki da jin dadi, kafin ya bar wajen zuwa
kauyensu, ya yi addu’a, ya ce; “Ya Allah! Wanda babu wani abin bauta in
ba shi ba, ka ba Fatima abin da ido bai ta'ba gani ba, kuma kunne bai
ta'ba ji ba”.
Bayan haka, Ammar bin Yasir da ya sayi wannan sarka, ya sa mata turare na Almiski ya nade ta a wani kyalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (Saww). sarkar da Bawan, duk ya ba shi.
Daya isa wajen Manzon Allah (Saww) ya fada masa sakon. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce je ka kai wa Fatima sarkar da wannan Bawa. Ya je wajen nana Fatima ta amshi sarkar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi.
Lokacin da Manzon Allah (Saww) ya ji haka sai ya yi
murmushi ya ce; “Wannan sarka mai albarka ta biya bukatar mabukaci (wato
Dattijo) ta kuma ‘yanta bawa, ta kuma koma hannun mai ita.
Bayan duk irin wannan kyauta da Nana fatima keyi Kuma bayan
kasancewarta 'yar Shugaban halitta (saww), amma gidan Mijinta Sayyidina
Aliyu (RA) Sai da hannunta yayi kanta akan aikin da take yi.
Nana fatima ta kasance me biyayyah Sau da kafa a gurin mijinta kuma ta kasance mai kyauta.
A rayuwar Sayyidina Aliyu (RA) yayi aure-aure amma bayan
rasuwarta, ba komai ya bata wannan matsayin ba face ayukkan da take na
alkheri tare da kyautatawa mijinta.
Babu shakkah ko kinada 'yar aiki yana da kyau ki ware wa
kanki wani girki wanda zaki rika dafawa mijinki da kan ki domin kara
daukaka darajarki a wajensa da kuma wajen Allah (swt).
Ya Allah ka karawa Nana Fatima daraja kuma ka yi jinkai ga sauran matan da suka kaikwayi halayenta.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
No comments:
Post a Comment