Thursday, 19 May 2016

CUTAR SIKILA (AMO SANIN JINI)

SIKILA (AMO SANIN JINI).
***********************

Cutace dake rayuwa a cikin jini mutum bil adama, cutar ana haihuwar mutum da ita ne, ma'ana cutace da ke zaune a cikin jinin jikin dan Adam.
Sikilar Wata cuta ce da ke kama jajayen kwayoyin halittu na jini. Wannan ciwo ba kwayoyin cuta ke kawo shi ba, gadonsa ake yi daga wajen iyaye, wadan da ke da wannan nakasar a kwayoyin jini.
Wasu mutanen, nakasar tasu rabi ce, wadanda ake wa lakabi da AS; wasu kuma duk kwayoyin a nakashe suke, wadanda su ne a ke kira da SS.
Cutar Sikila na daga cikin jerin ciwukan da sai dole an gada daga wurin mahaifiya da mahaifi sa’annan yake nunawa.

Jikin kowane 'dan adam yana dauke da wani abu da ake kira Genotype a turance. To wannan Genotype din idan har ya kasance na miji da mace su zo daya to kuwa 'ya'yansu duka zasu kasance ba masu cikakkiyar lafiya ba.

Akwai → AA wannan shine lafiyayye
Akwai → AS wannan  shine ke da rabin cutar (ma'ana bai munana ba).
Akwai → SS To wannan shine mai cikakkiyar cutar ta amosanin jini.

A lokacin duk lokacin da akayi aure tsakanin mai SS da SS to duka ’ya’yansu su gaji wannan nakasu (ma'ana zasu kasance masu dauke da Sikila din). Su dukansu da ’ya’yan nasu kuma kullum sukan kasance a cikin rashin lafiya, kenan rabin zaman auren za'a iya yinsa a jinyace.
A lokacin da mai ciwon (SS) ya auri mai rabin ciwon (AS), zai iya kasancewa wasu a cikin ’ya’yansu su gaji wannan ciwo.

Amma idan mai rabin ciwon (AS) ya auri wata mai rabin ciwon (AS), to rabin ’ya’yansu ne za su iya kasancewa masu amosanin jini, sauran kuma
lafiyayyu.

Duk lokacin da mai AA ya auri mai SS Ko AS to za'a iya samun sauqi kwarai da gaske.
Amma Idan Mai (AA) ya auri mai (AA) to fa shikenan babu zance haduwa da 'ya'ya masu dauke da cutar ta Amosanin jini.

KO CUTAR TA SIKILA KALA DAYA CE?
A'a Cutar ta Sikila kala 3 ce; Akwai mai sa kumburin gabobi.
Akwai mai shanye jini gaba daya sai an rika yi ana sanyawa mutum jini.
Akwai kuma mai sa zazzabi mai tsananin gaske, a rika ganin mutum ko yaro yau ciwo gobe lafiya.

TO ANA WARKEWA DAGA WANNAN CUTAR?
A likitance babu maganin da ke warkarda wannan cutar kasance wa cutace da take manne da jini kuma cuta ce da take tare da jini a koda yaushe.
Amma a musulunce tabbas akwai maganin da ke warkar da wannan Cuta ta Sikila Domin Allah (SWT) ya fada Cewa, Bai saukar da Cuta ba sai da ya saukar da maganinta.
Don haka ga masu Sikila ko 'ya 'ya masu Sikila ko 'yan Uwa masu Sikila ga Magani daga ZAUREN-MANAZARTA da Iznin Allah.

Za'a nemi Ganyen Zogala a tare da Tare da zangarniyar Zogalan a hade waje guda a markade a rika shan rabin karamin Kofi sau 2 a rana tsawon wata 2 In shaa Allahu za'a yi mamaki.
Muna Rokon Allah ya biyawa kowa bukatarsa ya warkarda majinyatan mu.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

No comments:

Post a Comment