Saturday, 23 January 2016

SAKO ZUWA GA MATAYENMU

SAK'O ZUWA GA MATAYE MU

Kafin Zuwan Manzon Allah (saww), anyi wata baiwar Allah mai fasaha UMMAH Bint Al-HARIS ita wannan matar ta kasance 'yar Kabilar BANIY SHAIBAN ce.

Sunan Mijinta AUFU bin MUHALLAM AS-SHAYBANIY shi wannan Miji nata ya kasance shugaba (Sarki) ne a cikin Kabilar su kuma shine jagoransu. Suna da wata 'ya mai suna Ummu-iyaas, sai sarkin wani gari mai suna kinda sunan wannan sarkin kuwa Alharis Bin Amru ya nemi auren 'yarsu mai suna Ummu-iyaas, sai kuma aka aurar masa ita, to a nan ne mahaifiyar wannan amarya ta yi mata wasiyya da zamu gabatar muku a wannan ZAUREN-MANAZARTA.
Kuma wannan wasiya da yawa maluma suna daukanta daga cikin mafifitan wasiyyoyi da aka yi ma 'ya mace lokacin aurar da ita.

Wannan Matar ta Fara da Cewa, "Ya ke karamar 'yata! Lallai wasiyya da za'a iya barin gabatar da ita ga mutum don cikar ladabinsa to da baza a yi miki ita ba sai dai ita (wasiyya) tunatarwa ce ga wanda ya gafala, taimako ne ga duk mutum mai hankali. Da ace akwai matar da zata wadata ba sai ta yi aure ba; saboda kasancewar iyayenta mawadata, da kuma son da suke mata; To da ke ce kika fi dukkan mata bukatar barinsa (aure); sai dai kuma su mata an halicce su ne don maza, kamar yadda don su (matan) aka halicci maza!

Taci gaba da Cewa, ! !Ya ke karamar 'yata! Lallai ke kin riga kin rabu da wannan yanayin da kika fito daga cikinsa, kin kuma bar sabon da kika fito daga cikinsa (ma'ana: kin bar gidan da aka haife ki, sannan kika girma a cikinsa; gidan iyaye), kin tafi zuwa gidan da baki sanshi ba, zuwa kuma ga abokin zaman da baki saba da shi ba, wanda ya wayi gari za'a daura muku aure tare, zaki je ga wanda zai mallake ki; Don haka Ki zame masa baiwa (mai bin umurni) Ina kyautata zato idan kika zamar masa baiwa shi kuma zai zame miki bawa mai sauri amsawa Taci gaba da Cewa, Yake Karamar 'yata Ki ji sifofi goma daga gare ni; za su zame miki guzuri, kuma abin ambato a gidan miji;

NA FARKO DA NA BIYU: Ki yi abota da mijinki da wadatar zuci, ki kuma yi zamantakewa da shi cikin ji da biyayya. Ma'ana; Abota da wadatar zuci anan tana nufin duk abinda mijinki ya kawo miki kada ki kushe abin, ki zama mai godia a gareshi duk abinda ya kawo ko ya sayo miki.

NA UKU DA NA HUDU: Ki kiyaye mai idanunsa biyu zasu gani, da wanda hanci zai ji; kar ki yarda idanunsa su ganki kina aikata mummuna, kada kuma hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin iska!
Ma'anar Ki kiyaye me idanunsa biyu zasu gani anan, tana nufin, ta sanya ido akan abinda mijinta ke fara kallo idan ya dawo daga ofis ko kasuwa,

Idan kafafuwanki yake kallo ki tabbatar kafin ya dawo ke wanke su ke gyarasu sosai
Idan kuma Kirjinki yake fara kallo sai ki yawaita kula da shi ki masa abinda zai rika dad'a masa sha'awar kirjin.

Idan kuma fuskarki yake fara kallo to ki tabbatar ke tsaftace ta kafin ya shigo gidan.
Ma'anar kada ki bari idanunsa ya ganki kina aikata munana anan shine, Kada ki bari mijinki ya ganki kina satar masa kuddi da sauransu. Ma'anar Kada hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin iska anan shine, Kada ki bari mijinki yaji wani wari a jikin ki, ko a bakinki ko a hamattanki da sassan wuraren da Wari ke fita.

NA BIYAR DA NA SHIDA: Kiyaye lokacin cin abincinsa, da kuma natsuwa a yayin barcinsa; saboda tsananin yinwa na kunna bakin-wuta, yayin da shi kuma yanke barci ke sanya bacin rai! Da tace, Ki kiyaye lokacin cin abincinsa, anan tana nufin Idan har yana jin yunwa to ki kula kada ki taso masa da wata maganar daban ko wani korafi (Complain) har sai kega ya ci Abinci ya koshi. Da tace, Ki natsu a lokacin baccin sa, anan tana nufin kada mijinki yana jin bacci kice zaki takura shi da surutu, ko kuma nuna biyan wata bukata.

NA BAKWAI DA NA TAKWAS: Ki kiyaye masa dukiyarsa, ki kuma kula masa da danginsa da iyalansa; saboda kiyaye masa dukiya na daga kyawawan siffofi, shi kuma lura da danginsa da iyalansa yana daga girmamawa Da tace, Ki kula masa da dukiyar sa anan tana nufin, Kada ki rika saka mijinki yana kashin kuddi da yawa. Ki kula da danginsa, anan tana nufin kada ki wulaqanta 'yan uwansa domin Wulaqanta dangin miji na saka suji sun tsani mijin, shi kuma daga karshe yaji ya tsane ki.

NA TARA DA NA GOMA: Kada ki yada sirrinsa, kuma kada ki saba ma umurninsa; saboda idan har kika yada sirrinsa to baza ki taba amintuwa da shi ba, in kuma ki ka saba umurninsa to kin tafasa kirjinsa!
Ma'anar Kada ki yad'a sirrinsa anan tana nufin, Kada mijinki ya gaya miki wani muhimmin sirri kije ki gayawa wata, domin idan har kika gayawa wata yaji to gobe zai rika gudun gaya miki wata magana.
Sai kuma ta cike wasiyyarta da fadin;

Ki kuma kiyayi yin farin ciki a lokacin da mijinki ke cikin bacin rai, da bayyanar da bacin rai a lokacin da yake farin ciki; saboda yin farin cikin mace lokacin bacin ran mijinta na daga sakaci da jafa'i, yayin da shi kuma bata ranta a halin farin cikinsa zai gurbata masa nasa farin ciki!

Kuma gwargwadon yadda kika kasance kike girmama shi, gwargwadon yadda zai yi ta karrama ki (da kyautuka), kamar yadda gwargwadon yadda kike masa muwafaka (ba gardama) gwargwadon jimawanki a wajensa!

Kuma ki sani! Ba za ki isa ga samun abinda kike so ba; har sai kin fifita yardarsa akan yardarki, da abinda yake karkata zuwa gare shi akan naki; cikin duk abin da kika so, ko kika ki!
Daga karshe ta rufe da Cewa, ALLAH YA YI MIKI ZABIN ALKHAIRI.

A Duba a DA'IRATU MA'ARIFIL USRATIL MUSLIMAH (littafi na 54/ shafi na 180).
Ya 'yan Uwayen mu mata ku lura da kyau da wannan Wasiya da kyau, hakika da duka matayen mu zasu kula da wayannan abubuwa da sun mallake mazajen su. In Shaa Allahu zamu kawo kwatan kwacin Wannan shawara zuwa ga Maza. Wannan Sakon Yana Bukatar Watsuwa Ga sauran 'yan Uwa da Fatar ALLAH zai baku Ikon Isarwa kamar yadda na Isar.

SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

www.facebook.com/zaurenmu Ko kuma zaurenmanazarta8@gmail.com

No comments:

Post a Comment