Saturday, 3 December 2016

DAGA BAKIN DA BAYA KARYA

DAGA BAKIN MA'AIKI (SAWW)
******************************
Manzo (Saww) yana cewa; Idan al’ummata ta aikata wasu abubuwa, to lalle bala'i zai fada masu, sai aka ce: Ya Manzon Allah (saww) Wadanne abubuwa kenan?
Sai ya ce: Idan dukiyar qasa ta zamanto mallakan wasu ‘yan tsiraru suna yin yadda suka ga dama da hana raunana amfanuwa da ita.
Amana kuma ta zama kamar ganima (ta yanda da an bawa mutum zai cenyeta).
Zakka ta zamanto tamkar tara (mutane su zama basa iya fitar da ita).
Mutum ya kasance mai biyayya ga matarsa tare da sabawa mahaifansa.
Mafi qasqancin daga cikin al’umma ya zama shugaba, amma al’umma suna girmama shi don tsoron sharrinsa. Da daga muryoyi a masallatai

Mutane su kasance suna Sanya alhariri (Tufan da ke bayyana jiki).
Bayyanar mata masu waqa kuma suke kada goge.
Na qarshen wannan al'umma su rika zagi da la'antar na farkonta.
To sai a saurari jar guguwa ko hadiyewar qasa ko shafewa.
Ya Allah kasa muyi kyakykyawan Karshe.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

No comments:

Post a Comment