Wednesday, 24 August 2022

MAGANIN BASIR

Mun sha yin bayani akan maganin basir amma har yanzu ina samun sako akan neman taimako game da basir, In shaa Allahu gashi.

Za'a nemi Garin Ruman a zuma acikin tatacciyar Zuma mara hadi a juyasu su hade sosai sai arinka shan karamin cokali 1 sau uku arana.

Wannan hadin maganin Yana Magani cutukka da Yawa kamar ulcer, basir, ciwon ciki, lalacewar ciki da sauransu.

Kuma Ya kansa, jikin mutum, yayi kyau Yayi karfi da Iznin Allah.

Allah ya kara mana Lafiya da Zama lafiya.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

www.fb.com/zaurenmu

Maganin Korar Aljani Kowane Iri

 MAGANIN KORAR ALJANI KOWANE IRI DAGA JIKINKA DAN ADAM.

Mun sha bayarda Wayannan Maganukka game da Aljannu a wannan Zauren, Ganin Bukatar haka muka ga sake gabatarda wannan Fa'idar domin taimakon Dalibbanmu na ZAUREN-MANAZARTA tare da sauran Al'ummar Musulmi duka.

Hanya ta Farko karanta wannan Addu'ar bayan kowace Sallah, tare da karantawa lokacin kwanciya hadi da lokacin da aka tashi daga bacci.

ﺍﻋﻮﺫ ﺑﻮﺟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ﻭﺑﻜﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﺎﻣﺎﺕ ﺍﻟﺘﻰ ﻻ ﻳﺠﺎﻭﺯﻫﻦ ﺑﺮ ﻭﻻ ﻓﺎﺟﺮ، ﻭﺑﺄﺳﻤﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺤﺴﻨﻰ ﻛﻠﻬﺎ ﻣﺎ ﻋﻠﻤﺖ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻟﻢ ﺃﻋﻠﻢ ﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺧﻠﻖ ﻭ ﺫﺭﺍ ﻭﺑﺮﺍ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﻨﺰﻝ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﻌﺮﺝ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﺫﺭﺍ ﻓﻰ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻣﺎ ﻳﺨﺮﺝ ﻣﻨﻬﺎ ﻭﻣﻦ ﻓﺘﻨﺔ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﻭﻣﻦ ﻃﻮﺍﺭﻕ ﺍﻟﻠﻴﻞ ﻭﺍﻟﻨﻬﺎﺭ ﺇﻻ ﻃﺎﺭﻗﺎ ﻳﻄﺮﻕ ﺑﺨﻴﺮ ﻳﺎﺭﺣﻤﻦ ﻭﻣﻦ ﺷﺮﻛﻞ ﺩﺍﺑﺔ ﺭﺑﻰ ﺍﺧﺬ ﺑﻨﺎ ﺻﻴﺒﻬﺎ ﺇﻥ ﺭﺑﻰ ﻋﻠﻰ ﺻﺮﺍﻁ ﻣﺴﺘﻘﻴﻢ .

TRANSLTRTION
****************
A'uzu bi wajhillahil karimi, Wabi kalimaatil lahil lati la yujawizuhunna barran wala fajiran, Wabi asma'illahil husna kulliha, ma alimtu minha Wa malam a'alam min sharri ma khalaqa, Wa zara'a wa bara'a, wa min sharri ma yanxilu minas sama'i, wa min sharri ma ya'aruju fiha, wa min sharri ma zara'a fil'ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariqan yaɗruqu bikhairin ya Rahmanu. Wa min sharri kulli dáabbatin Rabbi akhixun bi
nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin Mustaqim.

FASSARA
**********
Ina neman tsaruwa da Zatin Allah Mai Daraja kuma da cikakken kalmominsa, waɗanda babu wani na kirki ko fajirin da zai Qetaresu, kuma da sunayen Allah kyawawa dukkansu waɗanda na sani daga cikinsu da waɗanda ban sani ba, daga
sharrin abinda Ya halitta, kuma Ya fitar kuma Ya Qaga, kuma daga sharrin abinda yakan sauka daga sama, da kuma sharrin abinda ya kan hau cikinta, da kuma sharrin abinda ya fitar cikin ƙasa, da kuma sharrin abinda yakan fita daga gareta, kuma da fitinar dare da rana, kuma daga masu isowa da dare da rana sai dai mai isowa wanda zai iso da Alkhairi, Ya Mai Rahama, kuma daga sharrin dukkan dabba wadda Ubangiji Ya riƙeta da makwarkwaɗarta, hakika kan Ubangijina yana bisa Tafarki Madaidaici.

Hanya ta Biyu kuma itace a nemi tsabar habbatus Sauda, sai a karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin wannan tsabar, sai a dinga hayaki a dakin da ke kwana.

Sannan a nemi Wayannan Mayukkan Mane Ha/sauda, Man Zaitun, Man Albabunaj, Man Man tafarnuwa a hadasu wuri daya a karanta ayoyin Ruqiya A ciki a rika shan Cokali 2 sau 2 a rana kuma a rika shafawa lokacin kwanciya.

In Shaa Allahu za'a dace da Iznin Allah, Aljani zai gudu bada shiri ba.

Ya Allah ka tsaremu daga Sharrin Aljannu Mazansu da Matansu.

MUNA FATAN ZAKU TAYAMU WAJEN WATSA WANNAN SAKON

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA whatsapp. +2347031960698

Saturday, 19 May 2018

INA MA'AURATA MASU HUSUMA?

INA MA'AURATA MASU HUSUMA?
*********************************
Babu Shakkah da yawa daga cikin Ma'aurata dayawa basu san hakkokin da shari'a ta rataya musu akan wuyansu.
Kuma Rashin Sanin wayannan Hakkokin su suke rura wutar gaba ko fada a cikin Gidajen Da yawa daga ma'aurata.
Farko fari kamata yayi ma'aurata su san hakkokin da ke kansu, su fahimci mene ne sharia ta dora akansu tun gabanin akai ga zamantake war Auren.
In shaa Allahu ZAUREN-MANAZARTA zaiyi kokarin Zakulo wayannan Hakkoki domin dukan mu ma amfana dasu.
HAKKOKIN MATA MIJINTA.
-Daga Cikin Hakkokin Mata akan Mijinta akwai ciyarwa da tufatarwa.
Hadisi ya tabbata daga Sayyidina Abu Huraira (RA) ya ce: Manzon Allah (saww) ya ce, Dinaran da ka ciyar da shi fisabilillah, da kuma dinaran da ka 'yanta bawa da shi, da dinaran da ka ciyar da miskini da shi, da kuma dinaran da ka
ciyar da iyalinka, sai Manzon Allah (saww) ya ce, To, mafi girman lada a cikin wadannan shi ne dinaran da ka ciyar da iyalinka da shi.
Don Haka Yana da Yau Miji ya san Cewa, Ciyarda matarsa da iyalinsa yana bashi dinbin lada me yawan gaske.
Haka kuma Hadisi ya tabbata daga Mu’awiyyatul Kushairi (RA) ya ce Wata Rana Na Tambayi Manzon Allah (saww) Cewa, "Shin mene ne hakkin matar daya daga cikinmu a kansa? Sai Manzon Allah (saww) ya ce: ka ciyar da ita, idan ka ci, kuma ka tufatar da ita, idan ka tufata, kuma kada ka doke ta a fuska, kuma kada ka munana mata, kuma kada ka kaurace mata sai a cikin dakinta"
-Yana daga cikin hakkokin
mace a kan mijinta, ya rika yi mata kyakkyawan zato.
Domin mummunan zato shi ne yake kawo rashin zaman lafiya da rigingimu a cikin gida. Sai dai idan abin da yake zaton ya bayyana, ko kuma ya dogara da wata babbar hujja da zai kare kansa a nan duniya da kuma gobe Qiyama.

MUTANE 3 DA BAZA SU SHIGA ALJANNA BA

MUTANE 3 DA BAZA SU SHIGA ALJANNA BA
*************************************
Abdullahi Bin Umar (RA) Yace, Manzon Allah (saww) Yace, Mutum 3 Ba zasu shiga Aljanna ba, Sannan kuma Allah (swt) ba zai dube su ba a ranar gobe Qiyama.
Na farko Mutumen da baya yiwa Mahaifansa Biyayya, Na Biyu Matar da ta kwaikwayi maza, Na Uku Da kuma Dayooth Shima baya shiga Aljanna.
Dayooth, Shine mutumen da baya kishin Iyalansa (kamar, matarsa, mahaifiyarsa da kuma Qanne ko yayyensa Mata).
Imamu Ahmad Ya Ruwaito Shi.
Ya Allah ka tsare dalibban Zauren-Manazarta da su da dukkan Musulmi da Fadawa a cikin daya daga wayannan Mutane.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU

AYOYIN RUQIYA MASU TSANANI GA ALJANNU
**************************************
Wayannan Ayoyin Sune ayoyin Da Aljannu basa so, haka kuma wannan ayoyi waraka ne Ga kowane ciwo.
1. SURATUL FATIHA: Ankarbo hadisi daga Kharijah dan sult daga baffansa yace: Nazo gun Manzon Allah (saww) nayi masa sallama sai ya amsamin, sai na riski wasu mutane suna tareda wani mutum mahaukaci, sai dangin wannan mutumin suka cemin mun samu labarin abokinka (ko abokinku) yazo da
alkhairi, shin awurinka akwai wani abu da zaka yi ma wannan ya warke?
Sai yayi masa Ruqyah (addu'ah) da Suratul fatiha, sai Allah ya bashi lfy. Sai suka bani akuya, sai nazo Gun Annabi (saww) na bashi labari sai yace min Shin, ka Karanta wani abu  banda wannan Surah?
Nace a'a, sai yace min hakika kaci daga ruqyah ta gaskiyah, wato kayi magani da abinda shine mafi dacewa da inganci.
A duba a Abu-dawud hadisi mai
lamba 3420, da Nisa'i mai lamba 1032. Albani ya inganta wannan hadisin.
2. SURATUL BAQARAH : Annabi (saww) yana cewa:KADA KA
MAIDA GIDAJENKU MAKABARTA, DOMIN SHAIDANU BASA ZAMA GIDAN DA AKE KARANTA SURATUL-BAQARAH.
A duba a Sahihu muslim 6/67 da kuma Tirmizi 5/157.
3. SURATUL IKHLAS DA FALAQ DA NAS: An karbo daga Uqbatu dan Aamir (RA) yace, ina rike da
linzamin abin hawan Annabi (saww) a wurin wani yaki, sai yace min ya Uqbatu fadi! Sai na
saurari Annabi, sai ya kara cemin fadi ya uqbah!! Sai nayi shiru ina saurare, sai yakara
fada har sau 3, sai na ce mezan fada ya rasulullah (saww)?
Sai yace min ka karanta Qulhuwallahu ahada (har karshen surar ya karantamin) sannan falaq da nas har
karshe, da muka karanta su har karshe sai Annabi (saww) yace min: BABU WASU SURORI MASU
TSARI KAMAR WADANNAN).
A duba a Nisa'i Hadisi (8/250), Albani ya inganta hadisin.
Bayan wadannan Ayoyoin Babu shakkah ALKUR'ANI dukkansa Warakane, duk wata surah wadda take dauke da ambaton wani alkawari na ubangiji ko cika alqawari ga bayi sa, ko kuma ambaton wuta da aljannu da shaidanu kamar suratul Muminun,Yasin,Safat, Dukhan, Jinn, Hashr, Zalzalah, Qari'ah, Kafiruun, dasauransu duka ana karantasu wurin Ruqyah, musamman ga masu fama da
iska, ko sihiri.
DAGA CIKIN AYOYINDA AKE KARANTAWA YAYIN RUQIYAH DON WARAKA DAGA CUTUTTUKA NA SIHIRI, ISKA DA LALURA WADDA AKA KASA GANE MAGANINTA AKWAI:
-Ayata ta 36 cikin suratul fusilat.
-Ayatul kursiyyu (kamar yadda yazo akissar mutumin mai yiwa Abu-hurairah sata da daddare.(bukhar i 4/487)
-Ayoyi biyu na karshen Suratul baqarah,kamar yadda bukhari yafitar 6/323.
-Ayoyi ukku na cikin suratul A'raf (ayata 54 zuwa ta 56).
- Aya cikin suratu ali-imran (aya ta 18).
-Ayoyi hudu nacikin suratul muminun (ayata115 zuwa 118)
-Ayata ta 3 cikin suratul jinn.
-Ayoyi 10 na cikin suratus safat (ayata 1 zuwa 10).
-Ayata 21 zuwa ta 24 cikin suratul hashr.
-Ayata 31 zuwa ta 34 cikin suratul rahman.
-Ayoyi biyu nakarshen suratul qalmi (51 zuwa ta 52).
INSHA ALLAHU DUK WATA CUTA DA TA GAGARA MAGANI INDAI ANA KARANTA WADANNAN SURORI DA AYOYI ZA'A SAMU WARAKA.
IMAM IBN QAYYIM YACE: Duk wanda Alkur'ani bai warkar dashi ba to babu abinda zai
warkar dashi, Idan kuma Alkur'ani bai isar masa ba to babu wata isuwa da zai samu gun Allah.
Yaci gaba dace wa: Watarana ina a makka sai ciwo ya sameni sai na nemi mai magani na rasa bansamu wani magani ba da zanyi amfani dashi, sai na kasance ina yiwa kaina magani (ruqyah) da Suratul Fatiha sai naga tasirinta mai ban mamaki, nazamo ina dibar zamzam sai nakaranta fatiha na sha, sai gashi na samu waraka cikakka, har na zamo ina baiwa mutane magani akan hakan, kuma yana
amfanardasu.
Don Allah duk Wanda Ya Samu Wannan Rubutu ya tura shi a duka Contect dinsa da Groups dinsa ba tare da cire ko harafi daya ba (a rubutun) domin ya zamo sadakatur Jariya a garemu mu duka.
An Gabadar da wannan Darasi a Zauren-Manazarta Whatsapp tun Shekarar 2014 a watan August.
SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA Whatsapp

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

YADDA AKE TAZARAR HAIHUWA WACCE BABU WATA CUTARWA.

TAMBAYA TA 00113
********************
Salam, ALLAH ya gafarta Malam ina neman da ka taimaka ka sanar dani hanyar da AKE samun tazarar haihuwa a musulunce wacce bata da side effect bayan azalo, kamar yadda naga Kayi ishara da hakan a wani rubutu naka amma kace bazaka fasa ba saboda dalili Na Shari'a. ALLAH ya Sani ni da matata muna bukatar tazarar haihuwa saboda yanzu haihuwar ta hudu amma ko YAYE bata yi take samun wani cikin a takaice dai duk yaran hudu yanzu babu wanda ya iya yiwa kansa wani abu sai anyi masa kai hatta magana babu wanda cikin su ya iya sosai duk da cewa wannan halitta ce, in kuma gaskiya waccen hanyar bana sonta saboda side effect din ta, shi kuma AZALO duk Na gwada amma akwai sai mu wayi gari mu ga juna 2 ya shiga. Daga
jahiadmukhtar@gmail.com
AMSA
*******
Wa'alaykumus-Salam hakika tun lokacin da na kawo matsalolin allurar da ake yiwa mata domin tazarar haihuwa nake ta samu sakonni akan bukatar na bayyana wanda bashi da matsala a lafiyance.
Dalilin da yasa na ki bayyana shi a public saboda ban san ya abin zai kasance bane, domin nayi imani akwai daga cikin mata wayanda basa son su haihu da mazansu, akwai kuma wayanda nake tsoron su dauki abin suyi amfani da shi ta hanyar banza.
Amma in shaa Allahu yanzu zan gabatar da shi a bayyane, kuma ina rokon don Allah kada ayi amfani da shi ta hanyar da bata dace ba.
Da farko 'bangaren Namiji Idan yana bukatar tsayar da haihuwa zai nemi 'ya'yan Gwanda Ya rika cin su kullum har tsawon sati 3 to daga wannan sati 3 din in sha Allahu kwayayen da suke cikin maniyinsa zasu tsinke ta yanda ko sun hadu da kwayayen macce basu da karfin da zasu shigar da ciki.
Kuma zai ci gaba da cin 'ya'yan ne har sai lokacin da yake son maniyinsa ya dawo daidai, daga ya daina cikinsu kuma to shikenan kwayayensa zasu dawo lafiya qalau.
Ta 'bangaren Macce kuma za'a nemi Lemun tsami a hada da Ruwan lemu ayi matsi da shi kwana 5 da gama Al'ada in shaa Allahu a wannan watan ba zata 'dauki ciki ba.
Amma fa ina son ka sani komai kayi domin ka tsayarda haihuwa idan Allah bai so haihuwar ta tsaya ba sai an samu rabo.
Ina fatan zamu kula da kyau. In shaa Allahu da kadan kadan duk zan kawo ragowar dabarun tsayarda haihuwar.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
*********************************
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.
4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.
6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.