Saturday, 23 January 2016

SAKO ZUWA GA MATAYENMU

SAK'O ZUWA GA MATAYE MU

Kafin Zuwan Manzon Allah (saww), anyi wata baiwar Allah mai fasaha UMMAH Bint Al-HARIS ita wannan matar ta kasance 'yar Kabilar BANIY SHAIBAN ce.

Sunan Mijinta AUFU bin MUHALLAM AS-SHAYBANIY shi wannan Miji nata ya kasance shugaba (Sarki) ne a cikin Kabilar su kuma shine jagoransu. Suna da wata 'ya mai suna Ummu-iyaas, sai sarkin wani gari mai suna kinda sunan wannan sarkin kuwa Alharis Bin Amru ya nemi auren 'yarsu mai suna Ummu-iyaas, sai kuma aka aurar masa ita, to a nan ne mahaifiyar wannan amarya ta yi mata wasiyya da zamu gabatar muku a wannan ZAUREN-MANAZARTA.
Kuma wannan wasiya da yawa maluma suna daukanta daga cikin mafifitan wasiyyoyi da aka yi ma 'ya mace lokacin aurar da ita.

Wannan Matar ta Fara da Cewa, "Ya ke karamar 'yata! Lallai wasiyya da za'a iya barin gabatar da ita ga mutum don cikar ladabinsa to da baza a yi miki ita ba sai dai ita (wasiyya) tunatarwa ce ga wanda ya gafala, taimako ne ga duk mutum mai hankali. Da ace akwai matar da zata wadata ba sai ta yi aure ba; saboda kasancewar iyayenta mawadata, da kuma son da suke mata; To da ke ce kika fi dukkan mata bukatar barinsa (aure); sai dai kuma su mata an halicce su ne don maza, kamar yadda don su (matan) aka halicci maza!

Taci gaba da Cewa, ! !Ya ke karamar 'yata! Lallai ke kin riga kin rabu da wannan yanayin da kika fito daga cikinsa, kin kuma bar sabon da kika fito daga cikinsa (ma'ana: kin bar gidan da aka haife ki, sannan kika girma a cikinsa; gidan iyaye), kin tafi zuwa gidan da baki sanshi ba, zuwa kuma ga abokin zaman da baki saba da shi ba, wanda ya wayi gari za'a daura muku aure tare, zaki je ga wanda zai mallake ki; Don haka Ki zame masa baiwa (mai bin umurni) Ina kyautata zato idan kika zamar masa baiwa shi kuma zai zame miki bawa mai sauri amsawa Taci gaba da Cewa, Yake Karamar 'yata Ki ji sifofi goma daga gare ni; za su zame miki guzuri, kuma abin ambato a gidan miji;

NA FARKO DA NA BIYU: Ki yi abota da mijinki da wadatar zuci, ki kuma yi zamantakewa da shi cikin ji da biyayya. Ma'ana; Abota da wadatar zuci anan tana nufin duk abinda mijinki ya kawo miki kada ki kushe abin, ki zama mai godia a gareshi duk abinda ya kawo ko ya sayo miki.

NA UKU DA NA HUDU: Ki kiyaye mai idanunsa biyu zasu gani, da wanda hanci zai ji; kar ki yarda idanunsa su ganki kina aikata mummuna, kada kuma hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin iska!
Ma'anar Ki kiyaye me idanunsa biyu zasu gani anan, tana nufin, ta sanya ido akan abinda mijinta ke fara kallo idan ya dawo daga ofis ko kasuwa,

Idan kafafuwanki yake kallo ki tabbatar kafin ya dawo ke wanke su ke gyarasu sosai
Idan kuma Kirjinki yake fara kallo sai ki yawaita kula da shi ki masa abinda zai rika dad'a masa sha'awar kirjin.

Idan kuma fuskarki yake fara kallo to ki tabbatar ke tsaftace ta kafin ya shigo gidan.
Ma'anar kada ki bari idanunsa ya ganki kina aikata munana anan shine, Kada ki bari mijinki ya ganki kina satar masa kuddi da sauransu. Ma'anar Kada hancinsa ya shanshani wani abu face mafi dadin iska anan shine, Kada ki bari mijinki yaji wani wari a jikin ki, ko a bakinki ko a hamattanki da sassan wuraren da Wari ke fita.

NA BIYAR DA NA SHIDA: Kiyaye lokacin cin abincinsa, da kuma natsuwa a yayin barcinsa; saboda tsananin yinwa na kunna bakin-wuta, yayin da shi kuma yanke barci ke sanya bacin rai! Da tace, Ki kiyaye lokacin cin abincinsa, anan tana nufin Idan har yana jin yunwa to ki kula kada ki taso masa da wata maganar daban ko wani korafi (Complain) har sai kega ya ci Abinci ya koshi. Da tace, Ki natsu a lokacin baccin sa, anan tana nufin kada mijinki yana jin bacci kice zaki takura shi da surutu, ko kuma nuna biyan wata bukata.

NA BAKWAI DA NA TAKWAS: Ki kiyaye masa dukiyarsa, ki kuma kula masa da danginsa da iyalansa; saboda kiyaye masa dukiya na daga kyawawan siffofi, shi kuma lura da danginsa da iyalansa yana daga girmamawa Da tace, Ki kula masa da dukiyar sa anan tana nufin, Kada ki rika saka mijinki yana kashin kuddi da yawa. Ki kula da danginsa, anan tana nufin kada ki wulaqanta 'yan uwansa domin Wulaqanta dangin miji na saka suji sun tsani mijin, shi kuma daga karshe yaji ya tsane ki.

NA TARA DA NA GOMA: Kada ki yada sirrinsa, kuma kada ki saba ma umurninsa; saboda idan har kika yada sirrinsa to baza ki taba amintuwa da shi ba, in kuma ki ka saba umurninsa to kin tafasa kirjinsa!
Ma'anar Kada ki yad'a sirrinsa anan tana nufin, Kada mijinki ya gaya miki wani muhimmin sirri kije ki gayawa wata, domin idan har kika gayawa wata yaji to gobe zai rika gudun gaya miki wata magana.
Sai kuma ta cike wasiyyarta da fadin;

Ki kuma kiyayi yin farin ciki a lokacin da mijinki ke cikin bacin rai, da bayyanar da bacin rai a lokacin da yake farin ciki; saboda yin farin cikin mace lokacin bacin ran mijinta na daga sakaci da jafa'i, yayin da shi kuma bata ranta a halin farin cikinsa zai gurbata masa nasa farin ciki!

Kuma gwargwadon yadda kika kasance kike girmama shi, gwargwadon yadda zai yi ta karrama ki (da kyautuka), kamar yadda gwargwadon yadda kike masa muwafaka (ba gardama) gwargwadon jimawanki a wajensa!

Kuma ki sani! Ba za ki isa ga samun abinda kike so ba; har sai kin fifita yardarsa akan yardarki, da abinda yake karkata zuwa gare shi akan naki; cikin duk abin da kika so, ko kika ki!
Daga karshe ta rufe da Cewa, ALLAH YA YI MIKI ZABIN ALKHAIRI.

A Duba a DA'IRATU MA'ARIFIL USRATIL MUSLIMAH (littafi na 54/ shafi na 180).
Ya 'yan Uwayen mu mata ku lura da kyau da wannan Wasiya da kyau, hakika da duka matayen mu zasu kula da wayannan abubuwa da sun mallake mazajen su. In Shaa Allahu zamu kawo kwatan kwacin Wannan shawara zuwa ga Maza. Wannan Sakon Yana Bukatar Watsuwa Ga sauran 'yan Uwa da Fatar ALLAH zai baku Ikon Isarwa kamar yadda na Isar.

SAKO DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

www.facebook.com/zaurenmu Ko kuma zaurenmanazarta8@gmail.com

KIWON LAFIYA LOKACIN SANYI

KIWON LAFIYA A LOKACIN SANYI (Fitowa ta 1)
Babu shakkah akwai wasu abubuwan da ya kamata a kula dasu domin kula da lafiya a wannan lokaci na Sanyi.

1. Lokacin Sanyi lokacine da mutane manya da Kanana ke fama da mura, domin neman waraka daga mura za'a nemi Lemun tsami kamar kwaya 3 haka a matse shi sai a nemi zuma kimanin gwangwani daya a hadesu, daganan sai a kade idan aka kade sai a rika sha.
Manya Cokali 2 sau 3 a rana, yara kanana karamin cokali 1 sau 2 kullum, In shaa Allahu za'a dace.

2. Lokacin Sanyi Lokacine da Jikin Mutum ke yawan fitarda Vitamin C, kuma rashin wannan Vitamin din a jikin 'dan Adam yakan haifar masa da Bushewar fata, da leben baki (Lips), domin Samun Wannan Vitamin C din a jiki yana da kyau Mutum ya rika 'dan samu duk Safiya (misalin karfe 8 zuwa 9 daidai rana ta fara kaifi) ya rika dan gasa jikinsa a cikin rana na mintuna 30 ko ma 40 haka, In shaa Allahu jiki zai rika samun wannan Vitamin din.

A wasu Kasashe na Turawa da Larabawa musamman  Inda sanyi yayi Yawa sunada wurare da suka kebe domin gasa jiki da zafin rana. Allah ka Kara mana Lafiya.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.
FAMILY PLANNING (Qayyade yawan iyali) FOR COUPLES.

Yin Family planning Ba shi daga cikin manufar aure a musulunci, hakika bayan haramcin yinsa haka kuma yana tattare da Matsalolin masu dinbin yawa.
Allah ya fada a cikin Alqur'ani Cewa, “Kada ku kashe ‘ya’yanku don tsoron talauci, Mu muke azurta ku ku da ‘ya’yan naku.” 

Yahudawa maqiya addinin Allah ne suka kawo mana shi domin su rage yawan mu. Kuma duk
wanda ya ke bincike ya san qasashen da suke zuga mu da mu yi Family Planing su ba sa yi.
Lalle yana daga cikin ni’imar Allah ga dan Adam da Ya ba shi ni’imar ‘ya’ya, duk wanda ya yi aure bai samu da ba, to baya cikin kwanciyar hankali.

Abin da zai qara nuna mana mahimmancin ‘ya‘ya shi ne yadda Manzon Allah (saww) ya yi wa Anas bin Malik (RA) addu’ar Allah ya ba shi yawan ‘ya‘ya, Allah ya amsa addu’arsa ya ba shi ‘ya‘ya dari da ashirin
da biyar (125). Lalle wannan kadai abin yiwa nazarine.

Idan muka koma gun Manufar aure ita ce domin a hayayyafa
yadda manzon Allah (saww) zai yi alfari da yawan mu ranar kiyama kamar yadda yazo a hadisi Cewa, Wani mutumi ya zo wajen manzon Allah (saww)ya ce, “Ya RasulalLah na sami mata kyakkyawa ‘yar dangi amma ba ta haihuwa. Sai ya hana shi auren ta. Ya qara dawowa karo na biyu ya qara
maimaita maganar auren ta, amma Manzon Allah (saww) ya hana shi. Ya qara zuwa a karo na uku sai Manzon Allah (saww) ya ce masa, “KU AURI WADANDA KUKE SON SU SUKE SON KU Ku (wadanda suka iya soyayya) MASU HAIHUWA DOMIN IN YI ALFAHARI DA YAWANKU A RANAR TASHIN ALQIYAMA”.
Musulunci addinine mai tausayi da jinkai hakika Malaman musulunci sunyi qiyasi (yarda) akan tsarin iyali, amma da sharadi;
Na Farko, Ya zamana Mahaifiyar bata samun isasshen lokacin da zata shayarda jaririnta.
Na Biyu, Ya Zamana Mahaifiyar na shan wahala wajen haihuwa, anan an yarda ta tsaya ta huta.
Hakika ajiye haihuwa don tsoron talauci Haramun ne, Domin Allah (swt) yana Cewa, "KADA KU KASHE 'YA'YANKU DON TSORON TALAUCI, MU MUKE AZURTA KU KU DA 'YA'YAN NAKU".
Wasu sukan ajiye Haihuwa wai don a samu isasshen lokacin tarbiyantarda yara, hakika shima wannan ya sabawa koyarwar Manzon Allah (saww).
Domin Sayyidina Anas bin Malik (RA) ya shekara dari da hamsin (150) a duniya, saboda dadewa har sai da ya makance. Yana cikin makantar tasa ne ya kira babbar ‘yarsa mai suna Umainatu ya tambaye ta yawan
‘ya’yansa. Sai ta ce sai an qirga. Da aka qirga ne aka samu dari da ashirin da biyar kuma duk sun hardace Qur’ani. Shin idan yawan 'ya'ya na saka a kasa tarbiyan tarda 'ya'ya ya Sayyidina Anas ya yi da 'ya 'ya har guda dari da ashirin da biyar (125) kuma duk mahardata qur'ani? Babu shakka wannan kalubalene ga iyayen mu masu wannan rubarbar dabara.

YA MATSAYIN ALLURAR DA AKEYI DON HANA HAIHUWA (Contraceptive Injection)?
Ita wannan allurar ana kiranta da suna DMPA (Depot Medroxyprogesterone Acetate), wannan allurar ana yin tane duk bayan sati biyu (2morth), bincike ya nuna Idan aka yiwa macce wannan allurar galibi tana tsayar da saukar kwai ne daga cikin cikin mahaifar macce (ovulation), wanda wannan kwain a al'adance duk wata yakan sauko idan ya hadu da maniya ya zama 'da idan kuma bai hadu da shi ba sai ya zama jini ya fito (jinin al'ada). To idan Wannan Allurar ta rike wayannan kwayakwayi shikenan kuma sai bayan sati biyu wannan maganin zai kare aiki, sai a sake yin wata.

Ga Jerin Matan da hadarine sosai ga rayuwar su yi wannan allurar.
1. Matan da Basa iya haihuwa da kansu sai an musu aiki.
2. Matan da a koda yaushe kan yi fama da matsalar Zubar jini.
3. Matan da suke dauke da Sankaran mama ko suka warke daga sankaran maman (Breast cancer).
4. Matan da Suke da Borin jini (Allergic reaction).
Gaba daya wayannan matan duk suka kuskura suka yita zata kara janyo musu matsala.
Haka matar da take lafiya Qalau idan tayi wannan allurar idan har ba Allah ya tsareta ba zata iya kamuwa da wayanna matsalolin;
1. Yawaitar Zubar jini akai akai, ko kin daukewarsa gaba daya.
2. 'Daukewar jini gaba daya.
3. Rashin haihuwa har abada.
4. Sanya Breast Cancer.
5. Yawaitar Fitar Ruwa a gaban macce.
6. Matsalar kasusuwa (bone thinning) da sauransu.

Bayan wannan Allurar akwai maganin da ake sha hadi da wata roba da ake sanyawa.
Hakika bincike ya nuna duk abinda wannan allurar ke Sanyawa suma sukan haifarda matsalar.
Akwai hanyar da Musulunci yazo da ita, Itace ta yin azallo (namiji ya janye al'urarsa a lokacin da zaiyi inzali), Wannan itace hanyar da sahabbai (RA) sukayi.

Bayan sa akwai wani na musulunci wanda An tabbatar baida Side Effect Sai dai Kuma ayi min afuwa ba zan fadesa ba saboda dalili na shari'a.

Ina Fatan Iyayen mu mata Zaku kula da kyau, na farko ki dubi haramcin abin, sannan ki dubi cutarwar da zai iya janyo miki ki hakura da shi. Ina Fartar Yanda na Isar muku da wannan Sakon Kuma Zaku isar a duka contect da Groups domin duka mu amfana, a guji cenja wani abu na wannan rubutu don Allah, Amana.
Masu neman Haihuwa Allah kabasu, Masu Ciki kuma Allah ya Sauke su lafiya.
www.facebook.com/zaurenmu ko kuma zaurenmanazarta8@gmail.com