Friday, 9 December 2016

KARIYA DAGA SHIHIRI

KARIYA DAGA SHIHIRI
***********************
Babbar hanyar kariya daga Shiri daga Sharrin muggan Aljannu shine kiyaye dokokin Allah (swt) da kuma Cin Halat tare da kaucewa Haram.
Bayan Wayannan Hanyoyin akwai Hanyoyi masu yawa na kariya daga Sihiri wayanda Qur'ani da Hadisai sukazo dasu.
Babu Shakkah Qur'ani Shine babban Kariya Daga Sharrin duk wani Mugun mutum da Aljan.
Hakika kiyaye zikirin safe da yamma da zikirin bayan sallah na farilla da zikirin shiga bacci da na tashi daga bacci da zikirin shiga gida dana fita daga gida da zikirin shiga bayan gida da fita daga ciki da duk wani nau'in zikiri yana daya daga cikin Kariya.
Ana so da Safiya idan mutum ya tashi daga bacci ya karanta Falaqi da Nas a lokacin, In shaa Allahu babu wani abu da Zai sameka a wannan Yinin.

Da kuma Karanta wannan Addu'ar "la'ilaha illallahu wahdahu lasharika lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shai'in kadir" Sau 100 a kowace safiya da kuma yamma.
Wahid Abdussalam Bali ya kawo hirarsu da wani Aljani a cikin littafinsa, sarimul battar shafi na 136 zuwa 137 Inda Yake Cewa, Wani aljani ne da yaso ya raba wani mutum da matarsa. Sai malamin ya umarci Aljanin da ya fita daga jikin matar sai aljanin yace zai fita amma da
shardi guda.

Sai malamin ya tambaye shi sahradin sai Aljanin yace zan fita in koma jikinka sai malam
yace wa Aljanin, ba damuwa ka fita daga jikinta ka ka komo jikina in zaka iya.
Nan take sai Aljanin ya fashe da kuka sai malamin ya tambaye shi mai yasa yake kuka? Sai Aljanin yace, "AI BABU WANI ALJANI DA YA ISA YA SHIGA JIKINKA YAU".

Sai Malamin Ya tambayesa saboda me? sai Aljanin yace, "Domin Ka karanta la'ilahaillallahu wahdahu
lasharika lahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shai'in kadir" Lalle ne Mu kula da Wannan Addu'ar Sosai da Sosai Domin Ni karan kaina na tabbatar da Hakan.

-Shin kana Samun Kasala Wajen Karanta Wannan Addu'ar? Idan har kana Samun kasala wajen Karantata Ga wani sauqi Zauren-Manazarta ya Samo ma.

Ka Nemi Man Zaitun da Garin haltit da Man Ha/Sauda da Ruwan kahl na tuffa sai ka Hadasu wuri guda Ka karanta Falaqi da Nasi tare da wannan Addu'ar a cikin hadin. Sai ka rika shafawa duk safiya da Marece In Shaa Allahu Allah zai tsareka daga duk wani Sharrin Mutum ko Aljan kuma Allah zai tsareka daga Sharrin Masihirta. Muna Rokon Allah ya karemu daga duk wani abinqi.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

Saturday, 3 December 2016

DAGA BAKIN DA BAYA KARYA

DAGA BAKIN MA'AIKI (SAWW)
******************************
Manzo (Saww) yana cewa; Idan al’ummata ta aikata wasu abubuwa, to lalle bala'i zai fada masu, sai aka ce: Ya Manzon Allah (saww) Wadanne abubuwa kenan?
Sai ya ce: Idan dukiyar qasa ta zamanto mallakan wasu ‘yan tsiraru suna yin yadda suka ga dama da hana raunana amfanuwa da ita.
Amana kuma ta zama kamar ganima (ta yanda da an bawa mutum zai cenyeta).
Zakka ta zamanto tamkar tara (mutane su zama basa iya fitar da ita).
Mutum ya kasance mai biyayya ga matarsa tare da sabawa mahaifansa.
Mafi qasqancin daga cikin al’umma ya zama shugaba, amma al’umma suna girmama shi don tsoron sharrinsa. Da daga muryoyi a masallatai

Mutane su kasance suna Sanya alhariri (Tufan da ke bayyana jiki).
Bayyanar mata masu waqa kuma suke kada goge.
Na qarshen wannan al'umma su rika zagi da la'antar na farkonta.
To sai a saurari jar guguwa ko hadiyewar qasa ko shafewa.
Ya Allah kasa muyi kyakykyawan Karshe.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

MATSALAR KANKAN CEWAR AL'AURA

MATSALAR AL'AURA KARAMA.

TAMBAYA TA 00117
*********************
sallama irin ta addinin musulunci zuwa ga wannan zaure mai albarka. Da fatan alkairi. Dan Allah malam ina da tambaya: Ni shekara ta talatin tunda na taso na ganni da karamar al'aura, amma idan inajin sha'awa sai inga al'aurar tawa ta dan kara girma. shin malam wannan cuta ne? ko kuma halitta ta ce haka? idan kuma cuta ce, to dan Allah malam meye mafuta? Aure na ya kusa zuwa. Allah Ya kara
basira Ya kuma albarkaci wannan zaure da masu temakawa al'umma acikin sa.
AMSA
*******
Meye Sallama irin ta addinin musulunci? Kuma baka furta sallamar ba? Ya kamata mu rika girmama Sallama. domin itace kalami na farko da 'yan aljanna zasu yi.
Wannan ba cuta bane domin  masu binciken kimiyya da nazari akan al'aurar dan adam sun raba mutane maza zuwa gida uku game da girman al'aura.
Kason farko sune mutane na tsakiya (wato average) wajen yanayin girman al'aurarsu kuma
sune mutanen da akafi yawan samu.
Kaso na biyu sune mafi girman
al'aura (above average), wato sunfi na tsakiya girman al'aura.
Sai kuma Kaso na uku kuma sune na karshe wadanda suke da qasa da abinda kaso na 2 suke dashi (below average), wato masu karantar al'aura. To kai ina kyautata zaton wata kila kana daga cikin kaso na karshe (Masu karamar Al'aura).
kankantar Al'aura a lokacinda
yake kwance (flaccid length of penis) bashi bane abinda yake nuni da zahirin tsawonsa ba.
Domin kuwa mafi yawan mutane idan al'aurarsu tana kwance takan rage girma da tsawo ne. Amma daga zarar ya mike sai ya kara tsawo da girma.
Don haka wannan badamuwa bace. Ina rokon Allah ya amfanar da mu.
DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.