Wednesday, 9 March 2016

ZINA DA KASHE-KASHEN TA.
****************************
 A cikin Qur'ani Mai girma Allah (swt) yana gaya mana Matsayin wayanda basa yin Zina.
Allah (swt) yana cewa, (HAKIKA MUMINAI) SUNE MASU KIYAYE FARJINSU. SAIFA GA MATAYENSU, KO ABINDA SUKA MALLAKA NA KUYANGI, HAKIKA WAYANNAN BA ABIN ZARGI BANE. WANDA DUK YA NEMI (WANI ABU) KOMA BAYAN WANNAN WADANNAN SUNE MASU SHISSHIGI DA KETARE DOKOKIN ALLAH. (suratul Mumeen ayata 10)

Abin fahimta a cikin wannan ayar shine Allah ya bayyana cewa mace ba ta halatta ga mutum, sai ta wadannan hanyoyi guda biyu, ko dai aure na dindindin ko kuma mallakar kuyanga. Amma abin bakin ciki ayau har ire-iren zinace zinacen da ake yi a lokacin Jahiliya ana yinsu a yanzu. Ga dai kadan daga ire-iren Zinace-zinace da ake a lokacin Jahiliyya wanda har yanzu wasu daga cikin masu da'awar sun waye suke yi.

→ AUREN DADIRO:- Auren dadiro aure ne da mutanen Jahiliyya suke yi, wanda mutum zai rika soyayya da mace, ya ajiye ta yana zina da ita a boye, amma da zarar an gansu, to, ya zama haramun a wurinsu.
Wannan Aure yana daga cikin mafi munin nau’ikan zina, domin za a rika ganin mace ko namiji kamar salihai, bayan kuwa a boye tatatcen mazinaci, ko mazinaciya ce.
Da yawa daga cikin al'ummar musulmi a yau akwai wadanda suka mayar da matar dadiro tamkar matar aure, a kama mata daki a hamshakin hotel tare da kashe mata kudi fiye ma da yadda ake yiwa matar da ke gida. Lallai su sani cewa wannan mummunar dabi’a ce, su nisance ta domin karshen al’amarinsu ba zai yi kyau ba a nan duniya da kuma ranar gobe kiyama.

→ AUREN MUSANYAR MATA:- Auren musanyen mata aure ne shima da mutanen jahiliyya suke yi; mutum zai ce da wani mutum ka karbi matata, kai kuma ka ba ni taka matar, wato yana nufin ya ba shi matarsa ya rika saduwa da ita, haka shi ma ya ba shi tasa matar.
Abin mamaki, asalin musanyan mata mutanen jahiliyya ne suke yinsa ko kuma kasashen arna wadanda ba su san Allah da Manzonsa (saww) ba, amma sai ga shi yanzu wai a samu `ya`yan musulmi suna yinsa da nufin wayewar kai, wannan kuwa tabewa ce duniya da lahira, don haka masu aikata wannan mummunar dabi’a ya kamata su yi hattara kuma su tuba zuwa ga Ubangiji kada mutuwa ta riskesu.

→ AUREN NEMAN IRI:- Auren neman iri aure ne shima na jahiliyya wanda mutum zai tura matarsa ta je wurin wani mai mulki ko wani jarumi ya sadu da ita domin ta haifa masa da irinsa.
Kamar yadda Nana Aisha (rta) ta fada cewa, A zamanin Jahiliya Mutum ya kan tura matarsa idan ta tsarkaka (daga al’adar ta) sai ya ce da ita: ki je wurin wane ya sadu da ke, shi kuma mijin sai ya nisance ta, ba zai taba ta ba har sai cikinta ya bayyana, idan cikin ya bayyana, sai ya sadu da ita idan yana so, suna yin haka ne don kwadayin samun da (jarumi ko fasihi ko kyakkyawa d.s), to, wannan shi ake kira da auren neman iri…Wannan Auren yafi yawa a wajen Malaman Shi'awa, sukan tura matansu wajen Wani Babban Malaminsu don ya sadu da ita su samu da kamarsa (Allah ya tsare mu).

→ AUREN TARON DANGI:- Wannan shima aure ne na jahiliyya, wanda mutane uku zuwa goma suke auren mace daya a lokaci guda, kamar yadda ya tabbata a hadisin Nana A’isha (RTA) cewa, Akwai auren da mutanen jahiliyyya suke yi wanda mutum uku zuwa goma suke haduwa su auri mace daya suna saduwa da ita, idan kuma ta haihu sai ta kira su ta ce da su: kun san abin da kuke aikatawa da ni, to, a yanzu na haihu, sai ta jingina dan ga wanda take so daga cikinsu kuma babu wanda zai yi mata musu a kan hukuncin da ta yi. Wannan Auren ba'a cika yinsa ba anan nahiyar tamu sai a kasashen kamar su India da Napal da sauransu.

Akwai Kuma AUREN mutu'a wanda in shaa Allahu Bayanan sa zasu zo

Ina Rokon Ya Allah ka tsare mu daga fadawa cikin kowace irin zina.

Daga, ZAUREN-MANAZARTA.
www.facebook.com/zaurenmu

Monday, 7 March 2016

SHAWARORI TAKWAS GA MASU CIKI

SHAWARORI ZUWA GA MASU CIKI
******************************
***
Wayannan shawarori zasu amfani mata masu ciki sosai da sosai ta 'bangaren lafiyarki da jaririnki tare kuma da fatan samun na tsatstsen yaro.
 1. Yana da kyau Macce me ciki ta siffantu da halaye na kwarai tare kuma da gujewa munanen halaye.
2. Saurarar karatun Alqur'ani na mintuna 30 kullum ga macce mai ciki kan taimaka wajen samun natsatstsen yaro.
3. Kauracewa duk wani magani da ba likita ne ya bada umurnin a sha ba, kan taimaka wajen samun lafiyayen jariri.
4. Macce mai ciki ta guji rashin yin bacci da wuri, samun bacci na awa 8 kan taimaka wa kwakwalwar jaririn da za'a haifa.
5. Macce mai ciki ta guji aikin wahala ko kuma wani abu wanda yayi kama da shi domin samun lafiyar jikinta da ta jariri.
6. Mai ciki ta rika kula da abinci kafin taci, ta tabbatar baku tsakuwa ko datti a cikin abinda zata sha.
7. Yawaita cin kayan lambu irinsu, Zogale, Cucumber, kankana, lettuce, alayyahu da sauransu.
8. A karshe yana da kyau mai ciki ta rika cin dabino hudu a rana biyu da safe biyu da dare koma fiye da su.
Allah ya baku ikon saukewa, masu nema Allah ya basu, wayanda ke da Allah ya basu abin ciyarwa da ikon tarbiyantarwa.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

NANA FATIMA (RA) ABAR KOYI CE

MATA MU DAU DARASI DAGA NANA FATIMA (RA).
******************************
******************
Manzon Allah (Saww) ya ce, Fatima Shugabar mataye ce baki daya. Sai aka tambaye shi Maryam ’yar Imran fa? Sai ya ce, “Ita Shugabar Mata ce, amma na zamaninta.” ko kun san dalilin da yasa ta samu wannan matsayi da girma? To ku tsaya kuji.

An hadisi ruwaito daga Jabir bin Abdullahi Al’ansari (RA) ya ce; Mun yi Sallar Asar tare da Manzon Allah (Saww), bayan Sallah muna zaune tare da Manzon Allah (Saww), sai ga wani Dattijo ya zo ya je wajen Manzon Allah (Saww) yake yi masa bayanin halin da yake ciki na kunci na rayuwa na rashin abinci da tufafi da kuma kudi.Sai Manzon Allah (saww) ya ce masa; “Ga shi kuwa ba ni da wani abu da zan ba ka”
Sai ya ce masa; “Amma Ka tafi gidan Fatima”. Wannan Dattijo sai ya kama hanya zuwa gidan Sayyida Fatima (RA) da ya je gidan ya yi sallama.

Bayan haka ya shida wa Sayyida Fatima (RA) ga halin da yake ciki na bai da abinci da
tufafi da kuma kuddi. A lokacin da ya zo Nana Fatima ita ma ba ta da shi, saboda haka sai ta je ta dauko shimfidar da 'ya'yanta Hasan da Husain ke kwana, ta ce ga shi ya je ya sayar domin ya biya bukatarsa.
Sai Dattijon ya ce shi ba zai amsa ba, domin shi a tunaninsa abin ba zai yi kima ba. To kasantuwar ya raina wannan abin da aka ba shi, sai Nana Fatima ta shiga gida ta debe abin wuyanta, wato sarka, ta kawo masa.
Sai ya amsa, bai tsaya ko’ina ba sai wajen Manzon Allah (Saww), ya same shi yana zaune tare da Sahabbai, ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) Fatima ta ba ni wannan sarkar a kan in sayar domin in biya bukatuna”.
Nan da nan Sai Manzon Allah (Saww) ya fashe da kuka, ya ce yaya ko ba za ka samu biyan bukata ba, alhali Fatima ’yar Muhammad Shugabar mataye ta ba ka.

Sai Ammar bin Yasir (RA) ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ka ba ni izini in saye wannan abin wuyan”. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa yana iya saye Sai Ammar ya tambayi wannan Dattijon a kan nawa zai sayarmasa da sakar? Sai ya ce masa; “Ni daiabin da nake bukata kayan abinci da tufa ko da kuwa daya ne, da kuma Dinare, shi ma ko da daya ne da zai kai ni garinmu”. Sai Ammar ya hama masa kayayyakin abinci da kuma tufafi da kuma dabbar da zai hau zuwa garinsu, ya kuma ba shi kudi Dinare 20.
Bayan haka sai shi Dattijon ya zo wajen Manzon Allah (Saww), sai Manzon Allah (Saww) ya ce masa; “Ka samu abinci da tufan?” Sai Dattijon ya ce; “Ya Manzon Allah (Saww) ai ni yanzu na zama mawadaci”.
Saboda farin ciki da jin dadi, kafin ya bar wajen zuwa kauyensu, ya yi addu’a, ya ce; “Ya Allah! Wanda babu wani abin bauta in ba shi ba, ka ba Fatima abin da ido bai ta'ba gani ba, kuma kunne bai ta'ba ji ba”.
Bayan haka, Ammar bin Yasir da ya sayi wannan sarka, ya sa mata turare na Almiski ya nade ta a wani kyalle mai kyau ya ba Bawansa ya kai wa Manzon Allah (Saww). sarkar da Bawan, duk ya ba shi.

Daya isa wajen Manzon Allah (Saww) ya fada masa sakon. Sai Manzon Allah (Saww) ya ce je ka kai wa Fatima sarkar da  wannan Bawa. Ya je wajen nana Fatima ta amshi sarkar, shi kuma Bawan, ta ’yanta shi.
Lokacin da Manzon Allah (Saww) ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce; “Wannan sarka mai albarka ta biya bukatar mabukaci (wato Dattijo) ta kuma ‘yanta bawa, ta kuma koma hannun mai ita.

Bayan duk irin wannan kyauta da Nana fatima keyi Kuma bayan kasancewarta 'yar Shugaban halitta (saww), amma gidan Mijinta Sayyidina Aliyu (RA) Sai da hannunta yayi kanta akan aikin da take yi.
Nana fatima ta kasance me biyayyah Sau da kafa a gurin mijinta kuma ta kasance mai kyauta.

A rayuwar Sayyidina Aliyu (RA) yayi aure-aure amma bayan rasuwarta, ba komai ya bata wannan matsayin ba face ayukkan da take na alkheri tare da kyautatawa mijinta.

Babu shakkah ko kinada 'yar aiki yana da kyau ki ware wa kanki wani girki wanda zaki rika dafawa mijinki da kan ki domin kara daukaka darajarki a wajensa da kuma wajen Allah (swt).

Ya Allah ka karawa Nana Fatima daraja kuma ka yi jinkai ga sauran matan da suka kaikwayi halayenta.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

WASU MAGUNGUNNA MASU BAN MAMAKI

WASU MAGUNNA MASU BAN MAMAKI DAGA ZAUREN-MANAZARTA   
************************************************************************************
1. Karas (Carrot), Idan aka yanka Karas (gunduwa-gunduwa) aka dubi wajen da aka yanke din da kyau za'a ganshi kamar kwayar cikin ido. Babu Shakkah Bincike ya nuna Cin Karas na bawa ido kariya tare da inganta glashin na ido.

2. TUMATUR (tomato), Idan aka yanka tumaturi a cikin sa za'a ga yana dauke da gidaje guda hudu (4 chambers), Zuciyar dan adam ma haka tana dauke da wayannan gidajen guda hudu (4 chambers).
Bincike ya nuna tumatur yana Inganta Zuciya tare da samar da Jini a duka sassan jiki.

3. INABI (grape), 'ya'yan Inabi suna kama da Kwayoyin da suke cikin jini masu bada kariya ga garkuwar jiki.
Bincike ya nuna yawan shan 'ya'yan Inabi na taimakawa gangan jiki tare da hana yaduwar kwayoyin cuta.

4. 'YA'YAN BAURE (Figs) suna kama da 'ya'yan Maniyin 'da Namiji.
Bincike ya Nuna 'ya'yan Baure na gyara maniyin 'da namiji, tare da kara yawan 'ya'yan Maniyin.

5. GYADA (Walnut), Idan aka 'bara ta za'a tarar da ita kamar Kwakwalwa.
Bincike ya nuna yawan mu'amula da ita yana bude kwakwalwa tare da sanya saurin rike abu.
Allah a cikin Alqur'ani Mai girma yana Cewa, SHIN WACCE DAGA NI'IMOMIN UBANGIJI KUKE KARYATAWA? (Suratul Rahman aya ta 13).

Duk Inda kasan kake da rauni a jikinka, Kwakwalwa ce, Ido ne to ka jaraba amfani da wayannan za'a dace.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.

AMOSANIN JINI (SIKILA)

SIKILA (AMO SANIN JINI).
********************************

Cutace dake rayuwa a cikin jini mutum bil adama, cutar ana haihuwar mutum da ita ne, ma'ana cutace da ke zaune a cikin jinin jikin dan Adam. Sikilar Wata cuta ce da ke kama jajayen kwayoyin halittu na jini. Wannan ciwo ba kwayoyin cuta ke kawo shi ba, gadonsa ake yi daga wajen iyaye, wadan da ke da wannan nakasar a kwayoyin jini. Wasu mutanen, nakasar tasu rabi ce, wadanda ake wa lakabi da AS; wasu kuma duk kwayoyin a nakashe suke, wadanda su ne a ke kira da SS. 

Cutar Sikila na daga cikin jerin ciwukan da sai dole an gada daga wurin mahaifiya da mahaifi sa’annan yake nunawa. Jikin kowane 'dan adam yana dauke da wani abu da ake kira Genotype a turance. To wannan Genotype din idan har ya kasance na miji da mace su zo daya to kuwa 'ya'yansu duka zasu kasance ba masu cikakkiyar lafiya ba.

Akwai → AA wannan shine lafiyayye
Akwai → AS wannan  shine ke da rabin cutar (ma'ana bai munana ba).
Akwai → SS To wannan shine mai cikakkiyar cutar ta amosanin jini.

A lokacin duk lokacin da akayi aure tsakanin mai SS da SS to duka ’ya’yansu su gaji wannan nakasu (ma'ana zasu kasance masu dauke da Sikila din). Su dukansu da ’ya’yan nasu kuma kullum sukan kasance a cikin rashin lafiya, kenan rabin zaman auren za'a iya yinsa a jinyace.

A lokacin da mai ciwon (SS) ya auri mai rabin ciwon (AS), zai iya kasancewa wasu a cikin ’ya’yansu su gaji wannan ciwo. Amma idan mai rabin ciwon (AS) ya auri wata mai rabin ciwon (AS), to rabin ’ya’yansu ne za su iya kasancewa masu amosanin jini, sauran kuma Lafiyayyu.

Duk lokacin da mai AA ya auri mai SS Ko AS to za'a iya samun sauqi kwarai da gaske. Amma Idan Mai (AA) ya auri mai (AA) to fa shikenan babu zance haduwa da 'ya'ya masu dauke da cutar ta Amosanin jini.
KO CUTAR TA SIKILA KALA DAYA CE? A'a Cutar ta Sikila kala 3 ce; Akwai mai sa kumburin gabobi.
Akwai mai shanye jini gaba daya sai an rika yi ana sanyawa mutum jini. Akwai kuma mai sa zazzabi mai tsananin gaske, a rika ganin mutum ko yaro yau ciwo gobe lafiya.

TO ANA WARKEWA DAGA WANNAN CUTAR?
A likitance babu maganin da ke warkarda wannan cutar kasance wa cutace da take manne da jini kuma cuta ce da take tare da jini a koda yaushe.
Amma a musulunce tabbas akwai maganin da ke warkar da wannan Cuta ta Sikila Domin Allah (SWT) ya fada Cewa, Bai saukar da Cuta ba sai da ya saukar da maganinta.
Don haka ga masu Sikila ko 'ya 'ya masu Sikila ko 'yan Uwa masu Sikila ga Magani daga ZAUREN-MANAZARTA da Iznin Allah.

Za'a nemi Ganyen Zogala a tare da Tare da zangarniyar Zogalan a hade waje guda a markade a rika shan rabin karamin Kofi sau 2 a rana tsawon wata 2 In shaa Allahu za'a yi mamaki.
Muna Rokon Allah ya biyawa kowa bukatarsa ya warkarda majinyatan mu.

DAGA, ZAUREN-MANAZARTA.